Tsohon gwamnan Ondo ya faɗi ainihin dalilin da yasaya sake sauya sheka zuwa PDP
- Tsohon gwamnan jihar Ondo da ya sauka ya bayyana dalilansa na sake komawa PDP bayan ya barta tun shekarar 2018
- Dakta Olesegun Mimiko ya ce ya dawo PDP ne domin sake fasalinta da kuma shirya kwato mulki daga hannun APC
- Ya ce lokaci ya yi da kowane mamba zai tashi tsaye su haɗa kai su ceto Najeriya daga halin da ta tsinci kanta a yanzu
Ondo - Tsohon gwamnan jigar Ondo, Dakta Olusegun Mimiko, ya yi bayanin dalilan da suka sanya ya sake koma wa babbar jam'iyyar hamayya PDP.
Vanguard ta rahoto cewa Mimiko ya bar PDP zuwa jam'iyyar LP a shekarar 2018, sanna ya koma ZLP kafin daga bisani ya sake komawa PDP a shekarar da ta shuɗe.
Da yake jawabi a wurin taron masu ruwa da tsaki a Akure, babban birnin jihar Ondo, Dakta Mimiko ya ce:
"Na dawo jam'iyyar PDP ne domin mu yi aiki tare mu kori jam'iyyar APC kuma mu ceto ƙasar mu daga hanyar watsewa."
"Ba muna faɗar haka dom mu yi wa wani sharri bane, sai don mu yi aiki ba ji ba gani domin kayar da jam'iyya mai mulki mu dawo da mulki hannun mu kuma mu sake gina ƙasa."
Ta ya PDP zata iya samun nasara kan APC?
A cewar tsoohon gwamna, hakan zai yuwu ne kaɗai idan, "PDP ta kawar da duk wani banbanci, ta yi aiki tare kuma mu yi aiki da haɗin kai kan turbar da yan ƙasa ke so."
Bisa haka, Mimiko ya yi kira ga mambobin PDP a lungu da sakon ƙasar nan su haɗa kan su wuri ɗaya kuma su yi duk me yuwuwa wajen fatattakar APC a kowane mataki har da gwanatin tarayya, Tribune ta rahoto.
A wani labarin kuma Yan takarar shugaban ƙasa uku a PDP sun haɗa sabuwar tafiya, sun shirya kwace mulki a 2023
Yan takarar kujerar shugaban ƙasa uku karkashin inuwar PDP sun haɗa kan su, sun shirya yin sulhu domin kwace mulki a 2023.
Jiga-Jigan siyasar uku sun ziyarci gwamna Ortom na jihar Benuwai domin neman goyon bayansa.
Asali: Legit.ng