2023: An Siya Wa Bala Mohammed, Gwamnan Bauchi Fom Din Takarar Shugaban Kasa a PDP

2023: An Siya Wa Bala Mohammed, Gwamnan Bauchi Fom Din Takarar Shugaban Kasa a PDP

  • Wata kungiyar matasa masu goyon bayan gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ta siya masa fom din takarar shugaban kasa a PDP
  • Sanata Mohammed ya mika godiyarsa ga kungiyar inda ya yi alkawarin cewa idan aka zabe shi zai zama shugaban Najeriya na yan Najeriya baki daya
  • Jam'iyyar PDP reshen Jihar Bauchi ta bakin shugabanta ta ce tana tare da Bala Mohammed saboda irin salon mulkinsa abin koyi ne ga kowanne dan siyasa

FCT, Abuja - Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya shiga jerin masu neman tikitin takarar shugabancin kasa a jam'iyyar PDP.

Ya siya fom din takarar, yana mai cewa idan aka bashi damar lashe zaben cikin gida ya kuma ci zaben shugaban kasa zai zama "Shugaban Najeriya Na Yan Najeriya."

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: 'Abokan Tambuwal' Sun Siya Masa Fom Takarar Shugabancin Ƙasa

2023: An Siya Wa Bala Mohammed, Gwamnan Bauchi Fom Din Takarar Shugaban Kasa a PDP
2023: An Siya Wa Bala Mohammed Fom Din Takarar Shugaban Kasa a PDP. Hoto: Sanata Bala Mohammed.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bala Mohammed ya yi magana ne a ranar Alhamis, a Abuja, jim kadan bayan ya karbi fom din takarar zaben da wasu kungiyar matasa karkashin shugabancin GBAM suka siya masa, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Zan zama shugaba mai sauraron al'umma tare da hada kansu, Bala Mohammed

A cewar Bala Mohammed, gwamnatinsa za ta tabbatar hada kan yan kasa baki daya sannan za ta tabbatar dukkan yan Najeriya daga kowanne lungu da sako sun yaba da mulkinsa, rahoton Nigerian Tribune.

Yayin da ya yaba wa BAM saboda siyan masa fomin din takarar, Bala Mohammed ya ce zai tabbatar ba a bar matasa da mata ba a baya wurin samun madafun iko.

Ya ce jam'iyyar PDP ce mafi karfi a kasar da ma Afirka, Bala Mohammed ya kara da cewa zai zama shugaban mai sauraron yan Najeriya da biya musu bukatu.

Kara karanta wannan

Umahi Ya Ziyarci Buhari, Ya Ce Takararsa Na Shugabancin Ƙasa 'Aikin Allah' Ne

Ya yi wannan jawabin ne yayin da aka gabatar masa da fom din takarar inda ya ce zai saka wa yan Najeriya ta hanyar shugabanci nagari idan an zabe shi.

Ya gode wa shugabannin BAM-V karkashin shugabanta Kwamared Jibo Mohammed, ya kuma yi alkawarin cigaba da inganta rayuwar yan Najeriya.

2023: An Siya Wa Bala Mohammed, Gwamnan Bauchi Fom Din Takarar Shugaban Kasa a PDP
Bala Mohammed tare da mambobin Bam-V da suka siya masa fom din takarar shugaban kasa. Hoto: Sanata Bala Mohammed.
Asali: Twitter

Muna tare da Bala Mohammed saboda irin salon shugabancinsa, Hamza Koshe Akuyam

A jawabin godiyarsa, shugaban PDP na Bauchi, Alhaji Hamza Koshe Akuyam ya mika godiya ga BAM-V yana mai cewa babu shakka Bala Mohammed ba zai bawa yan Najeriya kunya ba.

Ya kuma jadada cewa PDP na Jihar Bauchi tana tare da Bala Mohammed a ko ina domin tsarin shugabancinsa abin koyi ne.

Yanzu abin da ke gaban mu shine neman goyon baya daga deleget yayin zaben cikingida, Jibo Mohammed

Tunda farko, shugaban BAM-V, Jibo Mohammed ya ce kungiyar ta fara kaman wasa amma cikin kankanin lokaci ta samu karbuwa a sassan kasar.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Gwamna Tambuwal ya gana da IBB da Abdulsalami, ya bayyana shirin ‘yan takarar PDP

Jibo ya ce mambobin kungiyar sun hada kai ne suka tara N40m don siyan fom din kuma yana mai farin cikin ganin sun cimma burinsu.

Ya ce abin da ke gabansu yanzu shine aikin neman kuri'a a jihohin Najeriya daga wakilai na jam'iyya yayin zaben cikin gida.

'Abokan Tambuwal' Sun Siya Masa Fom din Takarar Shugabancin Ƙasa

A gefe guda, wata kungiya mai suna abokan Tambuwal ta siya wa gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal fom din takarar zaben shugaban kasa a jam'iyyar PDP.

Kungiyar, karkashin jagorancin Aree Akinboro, sun siya fom din ne a ranar Alhamis a hedkwatar jam'iyyar da ke birnin tarayya Abuja, The Cable ruwaito.

PDP ta tsayar da ranar 28 ga watan Mayu domin zaben yan takarar da za su wakilci jam'iyyar a zaben na 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164