Sauya sheka: Kotu ta sanya ranar yanke hukunci kan karar da ke neman a tsige Dogara

Sauya sheka: Kotu ta sanya ranar yanke hukunci kan karar da ke neman a tsige Dogara

  • Mamba a majalisar wakilai ta kasa, Yakubu Dogara na tsaka mai wuya bayan PDP ta shigar da kara kan komawarsa APC
  • Jam’iyyar adawar ta bayyana cewa kamar yadda yake a kundin tsarin mulkin Najeriya, ya kamata a saka kujerar Dogara a kasuwa tunda ya sauya sheka
  • Bayan sauraron karar, babbar kotun tarayya da ke Abuja ta saka Litinin, 11 ga watan Afrilu a matsayin ranar yanke hukunci kan shari’ar

Abuja - Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta sanya ranar Laraba, 11 ga watan Afrilu domin zartar da hukunci kan karar da ke neman a saka kujerar Yakubu Dogara a kasuwa saboda sauya shekarsa zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Mai shari’a Donatus Okorowo, wanda ya saka ranar ya ce duk da cewar da farko an shirya yanke hukunci a yau, hakan bai kammalu ba, The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Mulkin Buhari ba komai bane face yaudara, dan takarar shugaban kasa na PDP

Sauya sheka: Kotu ta sanya ranar yanke hukunci kan karar da ke neman a tsige Dogara
PDP ce ta yi karar Dogara a gaban kotu: Rt. Hon. Yakubu Dogara
Asali: Facebook

Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da shugabanta na jihar Bauchi, Hamza Akuyam, ne suka shigar da kara a gaban kotu, Daily Nigerian ta kuma rahoto.

Dogara, kakakin majalisar wakilai, Atoni Janar na tarayya, INEC da APC sune wadanda ake kara a shari’ar mai lamba. FHC/ABJ/CS/1060/2020.

PDP ta bukaci kotun da ta sallami tsohon kakakin majalisar wakilan daga matsayin dan majalisa mai wakiltan mazabar Dass, Tafawa Balewa da Bogoro na jihar Bauchi kan sauya shekarsa zuwa APC.

A cewar masu karar, ya kamata a bayyana kujerar Dogara a matsayin wacca ba kowa daidai da sashe na 68(1)(g) na kundin tsarin mulkin kasa.

Dogara ya sauya sheka daga PDP zuwa APC a ranar 24 ga watan Yunin 2020 lokacin da ya gabatar da wasikar murabus ga shugaban jam’iyyar na unguwar Bagoro a jihar.

Kara karanta wannan

Sauya sheka: Gwamna Ayade zai san makomarsa ranar Juma'a a rikicin da ake don ya koma APC

Sauya sheka: Gwamna Ayade zai san makomarsa ranar Juma'a a rikicin da ake don ya koma APC

A wani labari makamancin wannan, babbar kotun tarayya da ke Abuja za ta yanke hukunci kan karar da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta shigar kan Gwamna Ben Ayade na jihar Cross River, a ranar Juma’a, 25 ga watan Maris, rahoton The Nation.

Jam’iyyar PDP ta hannun lauyanta, Emmanuel Ukala, SAN, ta shigar da wata kara mai lamba: FHC/ABJ/CS/975/2021 a gaban mai shari’a Taiwo Taiwo inda ta nemi a tsige gwamnan da mataimakinsa kan sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN), ta tattaro a ranar Talata, daga kotu ta 7, inda Mai shari’a Taiwo ke jagoranci cewa za a zartar da hukunci da jam’iyyar PDP ta shigar kan gwamnan Cross River da mataimakinsa a ranar Juma’a mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng