Akwai yiwuwar kotu ta tsige Shugaban Majalisa da ‘Yan Majalisa 15 da suka shiga APC a Imo

Akwai yiwuwar kotu ta tsige Shugaban Majalisa da ‘Yan Majalisa 15 da suka shiga APC a Imo

  • Wasu ‘yan majalisar dokokin jihar Imo sun sauya-sheka daga jam’iyyarsu bayan sun lashe zabe
  • Chibuzo Ekene da Mmerole Modestus sun yi karar duk ‘Yan majalisar da suka dawo jam’iyyar APC
  • Idan suka yi rashin sa’a, za su iya rasa kujerunsu kamar yadda aka yi a jihohin Ebonyi da K/Riba

Imo - Jaridar The Eagle ta rahoto cewa wasu daga cikin ‘yan majalisar dokokin jihar Imo sun shiga halin dar-dar domin su na iya rasa kujerunsu a kotu.

‘Yan majalisan jihar Imo 17 ne su ke fuskantar wannan barazanar a sakamakon sauya-sheka da suka yi tun a baya, su ka shigo jam’iyyar APC mai mulki.

Tun bayan zaben 2019 ake ta samun wasu ‘yan majalisa daga jam’iyyun adawa irinsu PDP, AA da kuma APGA, su na shiga APC, har ta karbi rinjaye a Imo.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Kotu ta kwace kujerun wasu yan majalisa 20 saboda komawa APC

Daily Trust ta ce kujerun ‘yan majalisan su na girgidi ne bayan ganin Alkali ya tsige Gwamna Dave Umahi da duk ‘yan majalisan da suka bi shi zuwa APC.

Bayan nan kuma sai aka ji wata kotu ta tube ‘yan majalisar dokokin jihar Kuros Riba 20 a sanadiyyar barin jam’iyyar PDP da ta ba su kujerun da suke kai.

Ganin yadda hukuncin kotu suke gudana, wasu mutane sun shigar da kara a gaban Alkali, su na neman a tunbuke ‘yan majalisar dokokin da suka sauya-sheka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majalisar Imo
Majalisar dokokin jiha Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

An je gaban kotu

Jaridar ta ce Chijioke Nwachukwu, Chibuzo Ekene, da Mmerole Modestus ne su ka kai karar.

Ragowar su ne Ministan shari’a na kasa, tsohon shugaban majalisar dokokin jihar Imo da mataimakin shugaban majalisa mai ci da ‘yan majalisa 15.

Kara karanta wannan

Bikin sauya sheka: Tashin hankali yayin da jiga-jigan PDP 70 suka sauya sheka zuwa APC

Collins Chiji, Amarachi Iwuanyanwu da sauran abokan aikinsa za su kare kansu a gaban kotun tarayya da ke Owerri a kara mai lamba ta FHC/Ow/27/2020.

Lauyan da ya shigar da kara, Nath Epele, yana mai rokon a tunbuke ‘yan majalisar daga kujerunsu tun da sun sauya sheka daga jam’iyyun da suka ba su nasara.

Hon. Collins Chiji ya bar jam’iyyar APGA da ta sa mutanen Isiala Mbano suka zabe shi, ya koma APC mai mulki saboda burin zama shugaban majalisar jihar.

Wadanda za ayi shari’a da su a kotu sun hada da babban lauyan gwamnatin Imo kuma kwamishinan shari’a na jiha da hukumar zabe na INEC.

Wadanda suka bar jam’iyyar AA

A baya an ji cewa ‘Yan majalisar da suka yi watsi da jam’iyyar AA su ne; Uju Onwudiwe, Ngozie Obiefule, Johnson Duru, Arthur Egwim, da Obinna Okwara.

Sai kuma Heclus Okoro da shugaban majalisar dokokin jihar Imo mai-ci, Rt. Hon. Kennedy Ibe.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai sabon hari Zamfara, sun sheke dagacin kauye da wasu mutum 19

Wadanda suka fice daga APGA

Amara Iwuanyanwu, Chidiebere Ogbunikpa, Paul Emeziem, Ekene Nnodim da Onyemaechi Njoku ne suka bar APGA. Ku na da labari da farko sun fara shiga PDP.

Daga PDP zuwa APC

Rahotonni sun ce Kanayo Onyemaechi, Uche Oguag, Eddy Obinna da Samuel Otibe ne suka sauya-sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC mai rinjaye a majalisar Imo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng