Yanzu-yanzu: Yan majalisar dokokin jihar Imo 9 sun koma APC

Yanzu-yanzu: Yan majalisar dokokin jihar Imo 9 sun koma APC

Yan majalisar dokokin jihar Imo guda tara sun sauya sheka zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) daga jam'iyyun Peoples Democratic Party PDP, All Progressives Grand Alliance APGA, da Action Alliance.

Kakakin majalisar jihar ya bayyana hakan a wasikar da ya karanta a zauren majalisa ranar Talata.

Ga jerin wadanda suka koma APC:

Authur Egwim (Ideato North) AA zuwa APC

Chyna Iwuanyanwu (Nwangele), daga PDP zuwa APC.

Chidiebere Ogbunikpa(Okigwe), daga PDP zuwa APC.

Obinna Okwara(Nkwerre), AA zuwa APC

Paul Emeziem (Onuimo) daga PDP zuwa APC..

Ekene Nnodimele (Orsu) APGA zuwa APC,

Johnson Duru(Ideato South), AA zuwa APC

Ngozi Obiefule (Isu) daga AA zuwa APC

Heclus Okorocha (Ohaji/Egbema) daga PDP zuwa APC.

Mun kawo muku rahoton cewa Mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Imo, Okey Onyekanma, ya yi murabus daga kujerarsa.

Dukkan wannan dambarwan siyasan ya biyo bayan hukuncin kotun kolin Najeriya da ta fititiki gwamnan PDP, Emeka Ihedioha, kuma ta baiwa na APC< Hope Uzodinma.

Kotun kolin ta alanta Hope Uzodinma na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) matsayin zakaran zaben gwamnan 9 ga Maris, 2019.

Dukkan Alkalan kotun kolin sun yi ittifaki a shari'ar da Mai shari'a Kudirat Kekere-Ekun ta karanto cewa an zagbewa jam'iyyar APC kuri'un rumfunan zabe 388 yayinda ake tattara sakamakon zaben jihar Imo.

Mai shari'a Kudirat Kekere Ekun tace bayan an hada kuri'un runfuna 388 da aka zabge a farko da kuri'un da yan takaran suka sami, dan takarar APC ya kamata ace hukumar INEC ta sanar matsayin zakaran zaben.

Saboda haka, ta yi watsi da sanarwan INEC na baiwa Emeka Ihedioha nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng