'Yan majalisa 6 sun sauya sheka zuwa PDP a jihar Imo
Yayin zamanta da ta gudanar a ranar Litinin da ta gabata, mambobi shida na majalisar dokokin jihar Imo sun sauya sheka zuwa babbar jam'iyyar adawa ta PDP.
'Yan majalisar da suka hadar da guda biyar na jam'iyyar AA da kuma guda daya na jam'iyyar APGA sun bayar da sanarwar wannan hukunci da suka yanke cikin wata rubutacciyar wasika zuwa ga kakaki da kuma mai riko da sandar iko ta majalisar.
Tare da yankin da suke wakilta a jihar Imo, 'yan majalisar biyar na jam'iyyar AA (Action Alliance) da suka sauya sheka zuwa PDP sun hadar da; Mike Iheanaetu (Aboh Mbaise), Victor Onyewuchi (Owerri West), Ken Agbim (Ahiazu Mbaise), Lloyd Chukuemeka (Owerri North) da kuma Bruno Ukoha (Ezinihitte Mbaise).
Kazalika, Chiji Collins mai wakilcin karamar hukumar Isiala Mbano a karkashin iinuwa ta jam'iyyar APGA na daya daga cikin 'yan majalisar shida da suka sauya sheka zuwa PDP.
KARANTA KUMA: Zaben 2019: Janye karar kalubalantar nasarar Buhari ta farantawa fadar shugaban kasa
Bayan gudanar da babban zaben kasa kawo wa yanzu, jam'iyyar PDP na da mafi rinjayen kaso a sabuwar majalisar dokoki ta jihar Imo. A halin yanzu PDP na da kimanin 'yan majalisa 19 cikin kujeru 27 da majalisar dokokin jihar Imo ta kunsa.
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng