Takara a 2023: Dan takarar shugaban ƙasa ya faɗi gaskiya kan kalaman baiwa ɗan kudu tikitin PDP
- Gwamna Tambuwal na Sokoto ya musanta rahoton dake yawo cewa yace ɗan kudu ba zai iya kawo wa PDP nasara ba
- A cewar gwamnan rahoton da ake ta yamaɗiɗi da shi ba na yanzu bane, dan haka mutane su yi fatali da shi
- A cewar sanarwar da kakakin Tambuwal ya fitar, ko kaɗan bai yi makamancin zancen ba yayin ganawa da tsofaffin yan majalisu
Sokoto - Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, ya musanta rahoton da ake yaɗawa cewa ɗan takara daga kudu ba zai iya kawowa PDP nasara a zaben shugaban kasa ba.
Gwamnan ya yi ƙarin haske kan kalaman da ake jingina masa game da tikitin takarar shugaban ƙasa a wata sanarwa da kakakinsa, Muhammad Bello, ya fitar a madadinsa.
Daily Trust ta rahoto gwamnan na cewa ba'a fahimci maganarsa ba na cewa gwamnonin kudu maso kudu ko wani ɗan takara daga yankin ba zai iya lashe kujerar shugaban ƙasa ba.
Sanarwan ta yi karin bayani da cewa:
"Baki ɗaya da kanun labarin da kuma masu bibiya sun yi gurguwar fahimta kuma hakan ya sa ba su gane ainihin ɓatar da su da aka yi ba."
"Babu wani wuri da gwamna Tambuwal ya yi magana ko wata sanarwa da ta shafi takwarorinsa na kudu maso kudu yayin ganawarsa da tsofaffin yan majalisu a Abuja yau."
"Tambuwal bai faɗi cewa jam'iyyar PDP ko wani takwaransa gwamnan Kudu maso kudu, ko ɗan takara daga kudu ba zai iya lashe zaɓen shugaban ƙasa ba."
Gwamna Tambuwal ya ƙara da cewa rahoton daɗaɗɗen labari ne kuma ya kamata mutane su yi fatali da shi, kamar yadda the nation ta rahoto.
A wani labarin kuma Jam'iyyar APC ta gamu da cikas, Wani babban ƙusa tare da dandazon mambobi sun koma PDP
Jam'iyyar APC mai mulki ta gamu da wani cikas a Kwara yayin da take shirin babban gangamin taro na ƙasa ranar Asabar.
Tsohon ɗan takarar gwamna kuma jigo a APC ya jagoranci dandazon masoya sun koma jam'iyyar PDP mai hamayya.
Asali: Legit.ng