Sabon Ƙalubale Na Jiran Kwankwaso Idan Ya Bar PDP Zuwa NNPP, Zai Ci Karo Da Abokan Takara 15
- Sakataren watsa labaran jam’iyyar New Nigerian People’s Party (NNPP), Ambasada Agbo Major ya ce akwai ‘yan takarar shugaban kasa 15 da ke son tsayawa karkashin jam’iyyar
- Ya kara da bayyana cewa akwai ‘yan takarar gwamna, sanata, ‘yan majalisar tarayya da ‘yan majalisar jiha da yawa da suke da burin tsayawa karkashin inuwar jam’iyyar
- Ambasada Agbo ya ce za su shirya gangamin jam’iyyar a ranar 30 ga watan Maris kuma za a yi gangamin ne a Abuja kamar yadda ya sanar da manema labarai
Abuja - A matsayin shirye-shiryen gagarumin zaben 2023 da ke karatowa, sakataren watsa labaran jam’iyyar New Nigerian People’s Party (NNPP), Ambasada Agbo Majo ya ce yanzu haka akwai ‘yan takarar shugaban kasa 15, masu takarar sanata, ‘yan majalisar tarayya da na jiha da dama da suke son tsayawa karkashin jam’iyyar.
Ambasa Agbo ya ce jam’iyyar tana shirin yin gamgamin ta na gaba daya kasar nan a ranar 30 ga watan Maris wanda za su yi a Abuja, Nigerian Tribune ta ruwaito.
Yayin yi wa manema labarai jawabi a ranar Talata a garin Abuja, sakataren watsa labaran ya ce NNPP tana shirin kawo gyaran da ba a tana kawowa ba a kasar nan.
Manyan ‘yan siyasa suna ta shiga jam’iyyar
Ya ce jam’iyyar ta fara jan manyan ‘yan siyasa da kungiyoyi kamar The National Movement (TNM), Kwankwasiyya Political Movement, kungiyar mata ‘yan kasuwa da ke Osun da Jihar Gombe, kungiyoyin matasa da sauran ‘yan siyasa da suka sauya sheka daga wasu jam’iyyun.
Kamar yadda Nigerian Tribune ta ruwaito, ya ce:
“A matsayin mu na ‘yan Najeriya, ya kamata mu rungumi NNPP, yanzu haka akwai masu takarar shugaban kasa guda 15 da sauran ‘yan takarar gwamna, sanata, ‘yan majalisu na tarayya da na jihohi.
“Kusan shekaru 22 da ake amfani da kundin tsarin mulki, ‘yan Najeriya suna da burin samun jam’iyyar da zata kawo hadin kai, ci gaba da kuma adalci a kasa. Gwamnatin baya ta gaza yi wa Najeriya abin da ya dace.
“Yadda yanzu mutane su ke ta gangamin komawa NNPP, wannan jam’iyyar ce zata zama amarya a demokradiyyar Najeriya. Manyan mutane da manyan kungiyoyi suna ta shiga jam’iyyar wanda hakan babbar nasara ce.”
NNPP tana maraba da masu son shiga
Ya ci gaba da cewa suna maraba da duk wanda yake shirin shiga jam’iyyar. Jam’iyyar ta yi taron ta na gundumomi, kananun hukumomi da jihohi, a jihar Imo Filato da Abuja ne kadai aka dakatar saboda wata hayaniya da ta auku.
NNPP ta bukaci hukumar zabe mai zaman kan ta, INEC akan ta kasance mai adalci wurin gudanar da zabe kuma ya kasance na gaskiya da gaskiya.
Agbo ya tsaya akan cewa wajibi ne a kirga kuri’un ko wacce mazaba kuma a fitar da sakamakon zabe na ko wacce gunduma.
Asali: Legit.ng