2023: Dole magajin El-Rufai ya kasance mai ilimi kamarsa, ba wai jahili ba, inji jiga-jigan APC

2023: Dole magajin El-Rufai ya kasance mai ilimi kamarsa, ba wai jahili ba, inji jiga-jigan APC

  • Kungiyar masu ruwa da tsaki na APC a jihar Kaduna sun bukaci shugabancin jam’iyyar da ta tabbatar da ganin cewa magajin Gwamna Nasir El-Rufai ya kasance mai ilimi
  • Tsohon babban mai ba El-Rufai shawara ta musamman, Dr Usman Ahmed Danbaba, ya ce zagayen ‘Zone One’ ne ya samar da gwamna na gaba
  • Danbaba ya ce yankin yana da mutane da suka cancanci hawa kujerar gwamnan Kaduna

Kaduna - Kungiyar masu ruwa da tsaki na jam’iyyar All Progressive Congress (APC) a jihar Kaduna sun yi kira ga shugabancin jam’iyyar da ta tabbatar da ganin cewa magajin Gwamna Nasir El-Rufai ya kasance mai ilimi sosai.

Sun yi bayanin cewa yana da matukar muhimmanci ga jihar ta samu mutum mai ilimi kamar El-Rufai domin ci gaba da kyawawan manufofin gwamnan, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Matsalar tsaro ta fatattaki Bayin Allah 700, 000 daga gidajensu a Zamfara inji Kwamishina

Da yake jawabi a madadin kungiyar a wani taron manema labarai a Kaduna, tsohon babban mai ba Gwamna Nasir El-Rufai shawara ta musamman, Dr Usman Ahmed Danbaba, ya ce zagayen ‘Zone One’ ya samar da gwamna na gaba.

2023: Dole magajin El-Rufai ya kasance mai ilimi kamarsa, ba wai jahili ba, inji jiga-jigan APC
2023: Dole magajin El-Rufai ya kasance mai ilimi kamarsa, ba wai jahili ba, inji jiga-jigan APC Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Ya kuma jadadda cewar yankin na da mutane masu tarin ilimi domin shiga tseren kujerar gwamna a karkashin jam’iyyar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, yankin arewacin Kaduna ba ta amfana daga kowani babban mukamin siyasa ba tsawon shekaru bakwai da suka wuce a gwamnatin APC a jihar.

Ya ce sanatan, mambobin majalisar wakilai shida, 11 daga cikin 12 na yan majalisar dokokin jihar, 7 daga cikin 8 na shugabannin kananan hukumomi daga yankin duk yan APC ne, rahoton Punch.

Sai dai kuma ya ce babu gwamna, mataimakin gwamna, ministoci biyu, shugaban jam’iyyar, sakataren jam’iyyar, shugabar mata, shugaban matasa ko wakilin jihar a APC ta kasa da ya fito daga yankin na ‘Zone One.’

Kara karanta wannan

CAN ga El-Rufai: Ka daina wani girman kai, ka amsa ka gaza a fannin tsaro

“Mun yarda cewa ya kamata a saurara sannan a mutunta ra’ayoyinmu da matsayarmu a zaben fidda gwani na jam’iyyarmu mai zuwa. Musamman, tunda ya shafi zabin wanda zai gaji shugabanmu, Mallam El-Rufai.
“Abune da kowa ya sani cewa yankinmu shine inda APC ta fi karfi a jihar, jajircewarmu sun yi fice a dukkan zabukan baya na 2015 da 2019 da zabukan kananan hukumomi da aka yi a kwanaki.”

Kungiyar ta kuma kara da cewa suna bukatar dan takara da ya cancanta, mai tafiya da kowa kuma wanda ya san manufofi da tsare-tsare na gwamnatin Gwamna El-Eufai.

Kaduna 2023: Dattijo Ya Kai Wa Sarkin Zazzau Ziyara, Yana Neman Tubarraki

A wani labarin, dan takarar gwamnan Jihar Kaduna, Muhammad Sani Abdullahi wanda aka fi sani da Dattijo ya kai ziyara ga Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli har fadar sa, yayin da ya ke ci gaba da kamfen, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Shugaban EFCC, Bawa, ya yi martani kan kamen tsohon gwamna, zargin cin zarafinsa a siyasance

Dattijo yarima ne ga masarautar Zazzau idan aka bi tsatson sa ta marigayi Sarkin Zazzau, mai martaba Alhaji Dalhatu Usman Yero, na Fulato-Borno da ya mulka Zazzau.

Yayin da ya je kamfen din na kwana biyu, Dattijo ya samu tubarraki da kuma addu’o’i daga Sarkin Zazzau a fadarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng