2023: Kokarin sulhu ya faskara, Jam'iyyar APC ta fara rushewa a Gombe, Sanata Goje
- Tsohon gwamnan jihar Gombe ya gargaɗi APC cewa matukar ba'a kawo karshen rikicin APC a jihar ba, babu inda zata je a zaben 2023
- Sanata Danjuma Goje ya ce jam'iyyar APC na kan hanyar tarwatsewa a Gombe, shiyasa mutane ke sauya sheka
- Tun a watan Janairu 2022, kwamitin sulhu na APC ta ƙasa ya jagoranci zama tsakanin bamgarorin biyu
Gombe - Tsohon gwamnan jihar Gombe, Sanata Ɗanjuma Goje, yace har yanzun APC na kan hanyar tarwatsewa saboda kokarin yin sulhu tsakanin ɓangarori biyu ya tsaya cak.
Goje, wanda ke zaune a kan kujerar Sanata, ya yi hasashen cewa APC ba zata iya taɓuka komai ba a zaɓe mai zuwa matukar ba'a haɗa kan ɓangarori biyu ba a jihar Gombe.
A wata sanarwa da Legit.ng Hausa ta samu ɗauke da sa hannun kakakinsa, Ahmed Isa, tsohon gwamnan ya ce dakatar da shirin sulhun barazana ce ga nasarar APC a babban zaben 2023.
Sanarwan ta ce:
"A matsayin masu son zaman lafiya a cikin jam'iyya, wadan da suka bada gudummuwa fiye da tunani wajen kafa tubali da gina jam'iyya har ta kai ga nasara a 2019, watsar da shirin sulhu na ɗinke ɓaraka ba abin da zai haifar sai rashin nasara a 2023."
"Idan haka ta faru, ka da mu ji wani ya zargi jagoranmu kuma uban gidanmu, Sanata Danjuma Goje, wanda duk da ciwan kan da mutanen da ya taimaka suka samu mulki suka ɗira masa, ya rungumi shirin.."
"Ya rungumi sulhu ne saboda haka Musulunci ya koya mana. Ka da mu yaudari kan mu, APC a Gombe na kan hanyar tarwatsewa kuma wajibi a shawo kan lamarin tun kafin dare ya yi."
A cewar sanarwan, matukar ba'a haɗa kan APC ba a Gombe to mulki ka iya suɓuce wa daga hannun jam'iyya.
Ina aka kwana game da batun sulhu?
Idan baku manta ba, Kwamitin sulhu karkashin jagorancin Sanata Abdullahi Adamu, bisa umarnin shugaban jam'iyya, Mala Buni, ya zauna da gwamna Inuwa Yahaya na Gombe da Sanata Ɗanjuma Goje.
Kwamitin ya gana da ɓangarori biyu na jam'iyyar APC a Gombe ranar 5 ga watan Janairu, 2022 domin kawo ƙarshen lamarin.
A taron wanda ya gudana a gidan Sanata Adamu na Abuja, an amince kowane tsagi zai jingine sabanin dake tsakaninsa da ɗan uwansa.
Haka nan kuma, za'a sake zama domin duba zaɓukan shugabannin da aka gudanar a matakin gundumomi. kananan hukumomi da jiha, domin adalci ga kowa.
Taron ya samu halartar shugaban kwamitin rikon kwarya na APC, Gwamna Mala Buni na Yobe, tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, Sanata Kashin Shetima, tsohon gwamnoni da Sanatoci.
A wani labarin kuma Kungiya a arewa ta lale miliyoyi ta siyawa Atiku Abubakar Fom ɗin takarar shugaban ƙasa a 2023
Kungiyar yan kasuwan arewa maso gabas sun lale miliyoyi sun karban wa Atiku Abubakar Fom ɗin sha'awar tsayawa takara a PDP.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya nuna tsantsar farin cikinsa tare da godiya gare su bisa wannan karamci.
Asali: Legit.ng