Tsohon Shugaban NEMA, Sani Sidi, Ya Koma PDP Bayan Shekaru 3 A Jam'iyyar APC
- Shugaban National Emergency Management Agency (NEMA), Alhaji Mohammed Sani Sidi, ya koma jam’iyya PDP daga APC
- Sidi ya bayyana batun sauya shekar ta shi ne a ofishin jam’iyyar na mazabar Kaduna ta tsakiya a karshen makon nan
- Kamar yadda tsohon dan takarar gwamnan a jam’iyyar APC ya ce, duk wanda ya bar gida, gida ya bar shi, hakan yasa ya kara komawa jam’iyyar
Jihar Kaduna - Tsohon darekta janar na National Emergency Management Agency (NEMA), Alhaji Mohammed Sani Sidi, ya bar jam’iyyar APC daga PDP, Nigerian Tribune ta ruwaito.
Sidi ya bayyana kudirin sa ne a ofishin PDP na mazabar Kaduna ta tsakiya a karshen makon nan.
Kamar yadda ya ce da tarin magoya bayan sa wadanda suka je ofishin cewa “duk wanda ya bar gida, gida ya bar shi. Ina farin cikin dawowa gida.”
Akwai bukatar ‘yan PDP su hada kai inji Sidi
Sidi, kamar yadda Nigerian Tribune ta nuna, tsohon dan takarar gwamna ne a jam’iyyar APC kuma ya shawarci duk wasu ‘yan PDP akan su hada kawunan su wuri guda don ganin ci gaban jam’iyyar a kananun hukumomi, jihohi da kuma kasa baki daya.
Yayin bayani akan burin sa na tsayawa takara, ya ce yanzu yana ta tuntubar manyan jam’iyyar da amintattun shi inda yace yana gab da sanar da kudirin sa.
Kamar yadda ya ce:
“Ba jita-jita ba ne, na sanar da kudirina na takara a gunduma ta. Yanzu ni dan PDP ne kuma na dawo gida ne daga jam’iyya ta. Ina ta tuntubar jagorori akan kudirina na takara.”
Ya samu rakiyar manyan mutane
Ya ci gaba da cewa:
“Akwai bukatar shugabanni da jagororin PDP su hada kai idan ba haka ba za mu fadi zabe. A matsayina na dan siyasa kuma dan PDP, akwai bukatar mu hada kai don ganin ci gaban jam’iyyar mu.”
Ya samu rakiyar tsohon kwamishinan kimiya da fasaha, Farfesa Dogara Mato, tsohon sakataren jam’iyyar PDP, Barista M. Aliyu da sauran su.
Asali: Legit.ng