PDP ta tausayawa matasa wajen biyan kudin fam din takara, ta rage masu 50% da wasu hukunci 11 da ta zartar
Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a ranar Laraba, ta amince da ragewa matasa kudin fam din takara a jam’iyyar da kaso 50 cikin dari.
A wata sanarwa dauke da sa hannun babban sakaten PDP, Debo Ologunagba, ya bayyana cewa dukka matasa da ke tsakanin shekaru 25 da 30 wadanda ke shirin neman takarar mukamai daban-daban za su biya kaso 50 cikin dari na kudin fam din takara.
Ologunagba a cikin wani jawabi da Legit.ng ta gano, ya bayyana cewa jam’iyyar ta yanke hukuncin ne a wata sanarwa cikin wata sanarwar da ta fitar a karshen taron kwamitin zartarwar PDP karo na 95.
A cewar Ologunagba, an gudanar da taron NEC din ne a sakatariyar jam’iyyar na kasa a Wadata Plaza da ke Abuja.
Sauran hukuncin da jam’iyyar adawar ta zartar gabannin babban zaben 2023 sune:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
1. NEC ta yaba da kokarin kungiyoyi daban-daban na jam’iyyarmu, kwamitin aiki na kasa, masu ruwa da tsaki na kasa, masu ruwa da tsaki na majalisar dokokin tarayya, kwamitin amintattu, kungiyar gwamnonin PDP da tsare-tsarenmu a matakai daban-daban wajen ganin an daidaita jam’iyyarmu don aikin da ke gaba.
2. NEC ya kuma yaba ma jajircewar uwar jam’iyya karkashin jagorancin Sanata Iyorchia Ayu na ci gaba da hada kawuna da sake fasalin jam’iyyar gabbanin babban zaben 2023.
3. NEC ya yaba ma uwar jam’iyya a kan nasarar jam’iyyar a zaben karamar hukuma a birnin tarayya da kuma zaben cike gurbi da aka yi kwanaki a fadin kasar.
Kwamitin ya kuma yaba ma uwar jam’iyyar kan gudnar da zaben fidda gwani na gwamnonin jihohin Ekiti da Osun cikin nasara sannan ya bukaci daukacin mambobin jam’iyyar da su jajirce don tabbatar da nasara a zabukan biyu.
4. NEC ya nuna karfin gwiwa cewa uwar jam’iyya za ta jagorantar jam’iyyarmu zuwa ga nasara a zaben shugaban kasa, yawancin gwamnonin jiha da kuma yawancin kujeru a majalisun dokokin tarayya da na jiha.
5. Kan halin da kasa ke ciki, NEC ta yi Allah wadai da rashin tsaro, rashawa da dukkan da rashin sanin yakamata na gwamnatin da APC ke jagoranta wanda ke haifar da tabarbarewar rashin tsaro da tabarbarewar tattalin arziki a kasar.
6. NEC ya kuma yi Allah wadai da kazamin cin hanci da rashawa da ake yi a gwamnatin APC, wanda ke haddasa matsalar man fetur da rugujewar ma’aikatar wutarmu ta kasa wanda ya gurgunta harkokin tattalin arziki da zamantakewa a kasarmu.
7. NEC ya bayyana cewa yan Najeriya na duba zuwa ga PDP don samun mafita sannan ya bukaci dukka mambobin jam’iyyar su ci gaba da hada kansu a kokarin PDP na ceto kasar da sake gina kasarmu daga mulkin zalunci na APC.
Shirye-shiryen zaben 2023:
8. NEC ya aimice da ka’idojin zaben PDP na gudanar da zaben fidda gwani
9. NEC ya amince da jadawali da ayyukan PDP na zaben 2023.
10. NEC ya amince da ragewa matasa da ke tsakanin shekaru 25 da 30 kudin fam din takarar mukamai daban-daban.
11. NEC ya kuma amince da fara siyar da fam din takara daga ranar Alhamis, 17 ga watan Maris, 2022.
12. Cikakken bayanin fam din da NEC ya amince da su sun hada da
Majalisar dokokin jiha
Ga majalisar dokokin jiha, fam din nuna sha’awar takara zai tafi kan N100,000 yayin da fam din takara yake a kan N500,000.
Majalisar wakilai
Ga masu takarar kujerar majalisar dokokin wakilai ta tarayya, fam din nuna sha’awar takara N500,000 ne yayin da fam din takara yake kan naira miliyan 2.
Majalisar dattawa
Masu hararar kujerar majalisar dattawa za su biya N500,000 na nuna sha’awar takara sannan naira miliyan 3 na fam din takara.
Gwamna
Yan takarar kujerar gwamna za su biya naira miliyan 1 na fam din sha’awar takara da kuma naira miliyan 20 na fam din takara.
Shugaban kasa
Masu son takarar kujerar shugaban kasa za su biya naira miliyan 5 na nuna sha’awar takara da kuma naira miliyan 35 na fam din takara.
Shirin 2023: PDP ta sa ranar zaben fidda gwani na 'yan takarar shugaban kasa
A gefe guda, mun kawo cewa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bayyana cewa ta kammala shirye-shirye domin gudanar da taron fidda dan takararta na shugaban kasa a zaben 2023 a watan Mayu.
A cewar wasu majiyoyi abin dogaro, ana iya gudanar da taron a ranar 28 da 29 ga watan Mayun 2022, jaridar Vanguard ta rahoto.
Da yake jawabi ga manema labarai a karshen taron majalisar zartarwa ta jam’iyyar a ranar Talata, sakataren labaran jam’iyyar na kasa, Debo Ologunagba, ya ce PDP ta kammala shiri tsaf domin babban zaben 2023.
Sauya sheka: APC na neman a hana Saraki, Tambuwal, Ortom da sauransu yin takara na shekaru 30 a sabon kara
Asali: Legit.ng