2023: Wani Ɗan Kasuwa Mazaunin Abuja Ya Shiga Jerin Masu Neman Gadon Kujerar Buhari a APC
- Wani dan kasuwa mazaunin garin Abuja, Dr Ibrahim Bello Dauda, ya shiga takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar APC na zaben 2023 da ke karatowa
- A ranar Talata, Dauda ya dauki alkawura da dama wadanda a cewarsa idan aka zabe shi zai cika su musamman don kawo ci gaba ga Najeriya
- A cewarsa, ya tsaya takarar ne sakamakon yadda mutane da dama suka takura masa bayan ganin ayyukansa, nasarorinsa da kokarinsa
Abuja - Wani dan kasuwa mazaunin birnin tarayya Abuja, Dr Ibrahim Bello Dauda, ya shiga jerin ‘yan takarar shugaban kasa wanda a zaben na 2023 karkashin inuwar jam’iyyar APC, Nigerian Tribune ta ruwaito.
Yayin bayyana kudirinsa a ranar Talata, Dauda ya yi alkawura daban-daban sannan ya fadi burinsa na bunkasa kasa, gyara shugabanci, kawo mafita ga matsalar tsaro, gyara a harkar ilimi da kuma samar wa mata gurbi a shugabancinsa.
Dauda ya ce ya tsaya takarar ne saboda yadda mutane suka tasa shi gaba akan lallai sai ya tsaya takara bayan ganin ayyukan da ya yi, dagiyarsa, kwazo da kuma kishin kasar sa.
Kamar yadda ya shaida:
“Kiran su ne ya sa na tsaya takara, da kudi na nake tallafa wa matasa don kawo ci gaba a duk inda na je cikin duniyar nan. Na yi matukar farin ciki da aka yi min wannan kiran kuma na amince zan tsaya takara a karkashin APC.”
Nigerian Tribune ta nuna inda Dauda ya yi magana akan irin salon shugabancin da zai yi.
Ya ce Najeriya zata ci gaba ta fannoni daban-daban na zamani. Kuma gaba daya duniya ma ta sauya, hakan yasa yake son kawo ci gaba ga Najeriya.
Zai kawo karshen rashin tsaro a kasar nan
A batun rashin tsaro, Dauda, wanda yaren Kanuri ne daga Jihar Maiduguri amma haifaffen garin Jos, ya ce:
“Daga Borno har Jos suna fama da rashin tsaro. Duk wanda zai duba Jos a halin yanzu, ba Jos din shekarar 1980 da doriya ba ce. Zai fahimci yadda tsaron ta ya tabarbare. Yanzu ta zama wuri mai hatsarin gaske.
“Sannan idan aka duba Jihar Borno, can ma babu irin ta’addancin da ba a yi. Mutanen Zamfara ba sa iya bacci cikin kwanciyar hankali.
“Mai zai sanya ‘yan Najeriya su dinga rayuwa cikin firgici a gidajen su? A bangaren kudu maso gabas kuwa ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda ne suka yawaita. Ga masu asirce-asirce.”
Zai tabbatar da walwalar jami’an tsaro idan aka ba shi dama
Ya ci gaba da kokawa akan rashin tsaro inda ya ce matsawar aka ba shi damar hawa mulki duk sai ya magance matsalolin.
Ya ce ya kamata ne a fara da wadata jami’an tsaro don su yi aiki yadda ya dace. Kuma zai tabbatar an sa musu ido don su zage damtse su yi aiki tukuru.
A cewarsa, zai tabbatar Najeriya ta hada kai da kungiyoyin kasashen ketare kamar NATO, AU da ECOWAS don hana shige da ficen haramtattun abubuwa kasar nan.
Dauda ya ci gaba da cewa za su tabbatar da walwala da karin kima ga ma’aikata, ciki har da ‘yan jarida.
2023: Wani Farfesan Najeriya Ya Yunƙuro, Zai Nemi Kujerar Buhari a Ƙarkshin Jam'iyyar APC
A wani labarin, wani Farfesa a Jami'ar Benin, Godspower Ekuobase, ya shiga jerin masu neman takarar shugabancin kasa a karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Daily Trust ta rahoto.
Farfesan ya gargadi yan Najeriya su guji karbar kudi daga hannun yan takara wadanda ba su da wani abin alheri da za su yi wa yan kasar sai dai su siya kuri'a daga bisani su wawushe kudin kasa.
Da ya ke magana da manema labarai a Benin, Jihar Edo, ya koka kan yadda yan Najeriya suke mayar da hankali kan yan siyasa masu kudi amma babu aikin da za su tsinana.
Asali: Legit.ng