Zaben 2023: PDP ta fara tattaunawa da tsoffin gwamnoni, yan majalisa da sauransu
- Jam’iyyar PDP na zawarcin wasu tsoffin mambobinta gabanin babban zaben 2023
- A yanzu haka shugaban PDP na kasa, Iyorchia Ayu na jagorantar wata tawaga ta jam’iyyar adawar domin tattaunawa da tsoffin gwamnoni, sanatoci da sauran manyan yan siyasa
- Wasu daga cikin manyan yan PDP da ake hange kan haka sune Sanata Danjuma Goje, Ibrahim Shekarau da yan majalisa da dama
Manyan mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) karkashin jagorancin shugaban jam’iyyar na kasa, Iyorchia Ayu, sun fara tattaunawa tare da tsoffin gwamnoni, sanatoci da mambobin jam’iyyar wadanda suka sauya sheka zuwa sauran jam’iyyun siyasa.
Jaridar The Nation ta rahoto cewa jam’iyyar adawar na kokarin karfafa kanta ne gabannin babban zaben 2023 mai zuwa.
An tattaro cewa tawagar ta PDP ta jera wasu tsoffin manyan mambobinta da suka koma wasu jam’iyyun siyasa.
Sauya sheka: APC na neman a hana Saraki, Tambuwal, Ortom da sauransu yin takara na shekaru 30 a sabon kara
Manyan yan siyasar da PDP za ta yi zawarci
Manyan yan siyasar da jam’iyyar ke zawarci don dawo da su PDP sun hada da tsoffin gwamnoni Danjuma Goje (Gombe), Adamu Aliero (Kebbi) da Ibrahim Shekarau (Kano).
Bugu da kari, jam’iyyar adawar na hararar sanatoci 22 da yan majalisar wakilai 50 wadanda ke a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a yanzu.
Rahoton ya kuma kawo cewa akwai hasashen cewa adadin na iya karuwa duba ga rikicin da ke gudana yanzu haka a jam’iyyar APC.
Wata majiya mai tushe ta bayyana cewa jam’iyyar PDP na amfani da rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar APC da rikicin da zai biyo bayan taron jam’iyyar da za a yi wajen janyo wasu ‘yan siyasa.
Daya daga cikin majiyoyin ta ce:
“PDP na yiwa APC yankan baya a jihohi da dama inda shugabanta na kasa, Dr. Iyorchia Ayu, ke jagorantar tattaunawa.
“Jam’iyyar adawar na amfani da rikicin APC, musamman kan rashin tabbass a babban taron jam’iyyar da kuma abun da zai biyo bayan zaben fidda gwani na shugaban kasa da gwamnoni. Yawan shari’ar da ake yi da APC abun tsoro ne.”
Siyasar Kano: Makusantan Kwankwaso sun lallaba sun gana da Shekarau, suna kokarin sake jawo shi PDP
A wani labarin, mun ji cewa siyasar Kano ta dauki sabon salo yayin da wasu manyan hadiman tsohon gwamnan jihar, Rabiu Musa Kwankwaso suka ziyarci Ibrahim Shekarau a Abuja a ranar Alhamis da ta gabata.
Majiyoyi sun bayyana cewa bakin na kokarin shawo kan babban abokin adawar ubangidan nasu domin ya dawo jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), wanda ya bari gabannin zaben 2019 saboda dawowar Kwankwaso jam’iyyar, rahoton Premium Times.
Shekarau ya koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ne bayan PDP ta mika shugabancinta a jihar ga Kwankwaso, wanda ya kasance dan jam’iyyar tun bayan kafata a 1998, har zuwa lokacin da ya koma sabuwar APC a 2014.
Asali: Legit.ng