Wani shahararren dan siyasar arewa ya fice daga APC, ya bayyana dalilinsa

Wani shahararren dan siyasar arewa ya fice daga APC, ya bayyana dalilinsa

  • Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Kaduna ta rasa wani babban jigonta
  • Samaila Suleiman, tsohon dan majalisar wakilai ya bayyana cewa ya sauya sheka ne saboda rabuwar jam’iyyar a matakin kasa
  • Sai dai kuma, Suleiman bai bayyana ko wacce jam’iyya zai koma ba bayan ficewar tasa

KadunaTsohon dan majalisar wakilai daga jihar Kaduna, Samaila Suleiman, ya sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Mista Suleiman, wanda ya wakilci mazabar Kaduna ta tsakiya a majalisar dokokin tarayya, ya ce ya yi murabus ne saboda zargin rabuwar kai a jam’iyyar a matakin kasa, Premium Times ta rahoto.

Wani shahararren dan siyasar arewa ya fice daga APC, ya bayyana dalilinsa
Samaila Suleiman ya fice daga APC Hoto: Mal. Samaila Suleiman Frontier Movement
Asali: Facebook

Sai dai kuma rahoton ya kawo cewa tsohon dan majalisar bai bayyana wacce jam’iyyar siyasa zai koma ba.

Mista Suleiman, a cikin wata wasika ta murabus da ya aike zuwa ga shugaban unguwa da karamar hukumarsa, ya ce:

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Makusantan Kwankwaso sun lallaba sun gana da Shekarau, suna kokarin sake jawo shi PDP

“Na rubuta a hukumance domin sanar maka da hukuncina na yin murabus daga matsayin mamba na APC.
“Wannan hukunci nawa ya zama dole saboda karya tsarin damokradiyyar cikin gida da rabuwar jam’iyyar a dukkan matakai, musamman a matakin kasa.
“Dan Allah ka sani cewa murabus din nawa ya fara nan take. Tare da wasikar ga lambar rijista na.”

APC ta gamu da gagarumin cikas a wata jihar kudu yayin da kansiloli 5 suka fice, sun koma PDP

A wani labarin, wasu yan majalisar karamar hukumar Obanliku a jihar Cross River su biyar sun sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa Peoples Democratic Party (PDP).

Labarin sauya shekar kansilolin biyar ya bayyana ne a karshen mako lokacin da aka gabatar da su a gaban mai neman takarar gwamna na PDP a jihar, Sanata Gershom Bassey, Thisday ta rahoto.

Kara karanta wannan

APC ta gamu da gagarumin cikas a wata jihar kudu yayin da kansiloli 5 suka fice, sun koma PDP

Kansilolin wadanda shugaban PDP a karamar hukumar Obanliku, Hon. Justine Ejisekpe, ya gabatar da su a gaban mai neman takarar gwamnan sune, Hon. Adida Justin, Hon. Ololo Francis, Hon. Helen Ejikang, Hon. Ogor Doris da Hon. Polycarp Ugiugbong.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng