Bukola Saraki ya bayar da gagarumin shawara ga ministocin Buhari
- Bukola Saraki ya bukaci wadanda ke rike da mukaman siyasa da su yi murabus daga kujerunsu kafin su shiga takarar kowani mukami
- Tsohon shugaban majalisar dattawan ya ce ba daidai bane wadanda ke hukumomin gwamnati su nemi takarar mukaman siyasa
- A cewar Saraki, sabon gyararren dokar zabe zai baiwa yan Najeriya damar zaben shugabanni da suka dace a manyan mukamai
Abuja - Tsohon shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki, ya yi kirfa ga masu rike da mukamai da ke neman yin takara a zaben 2023 da su yi murabus daga mukamansu na ministoci kafin su fara neman cimma burinsu.
Saraki ya kuma soki bukatar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aikewa majalisar dokokin kasar inda ya nemi a gyara sashi 84 (12) na dokar zabe.
Sashin ya haramtawa masu rike da mukaman siyasa yin zabe ko kuma a zabe su a yayin tarurrukan jam’iyya.
Ya ce babu dalilin da zai sa mutum ya ci gaba da kasancewa a kan kujerar mukamin da aka nada shi yayin da yake neman takarar wata kujerar siyasa.
Jaridar Punch ta rahoto cewa Saraki ya bayyana hakan ne jim kadan bayan ganawa da shugaban matasan PDP na kasa da shugabannin matasan jam’iyyar a matakin shiyya da jiha a sakatariyar jam’iyyar da ke Abuja.
Saraki ya ce:
“Ta yaya mutumin da ke rike da mukamin siyasa zai yi amfani da wannan damar wajen neman takara? Muna magana a kan shigowar matasa, wani dama matasan Najeriya ke da shin a yin takara a kan mutumin da ke zaune kan kujerar gwamnati, bayan yana da iko ga mulki, yana da iko ga kudaden gwamnati?
“Idan kana son yin takara, saboda Allah, ka yi waje, ka yi murabus sannan ka yi takara? Ta yaya za ka tsaya a ofishin siyasa? Ba daidai bane ma mu dunga yin muhawara a kan shi. Akwai son kai sosai.”
Saraki ya yi nuni da cewa sabuwar dokar za ta kara baiwa ‘yan Najeriya damar neman da kuma zaben shugabannin da suka dace.
Bakin alkalami ya bushe: An hana Buhari da Majalisa taba dokar da aka sa wa hannu
A gefe guda, babban kotun tarayya mai zama a garin Abuja ta hana shugaba Muhammadu Buhari da wasunsa wasa da sabon dokar zabe da aka shigo da shi.
A ranar Litinin, 7 ga watan Maris 2022, Mai shari’a Inyang Ekwo ya amince da karar da jam’iyyar PDP ta shigar, ya ce ba za a iya wasa da wannan doka ba.
Alkalin ya gamsu cewa tun da har kudirin gyaran zaben ya zama doka, ba za a iya kewaya shi ba. Wannan labari ya zo ne a jaridar Daily Trust dazu da safe.
Asali: Legit.ng