Sunaye: Gwamnoni, 'yan majalisar tarayya da jiha da za su iya rasa kujerunsu kan sauya sheka

Sunaye: Gwamnoni, 'yan majalisar tarayya da jiha da za su iya rasa kujerunsu kan sauya sheka

A ranar Talata, 8 ga watan Maris, babban kotun shari'a ta Abuja ta yanke wani hukunci da ya razanar, inda ta sauke Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi da mataimakin shi, Eric Igwe daga madafun iko, bisa sauya shekar da suka yi daga jam'iyyar PDP zuwa APC.

Alkali Mai shari'a Inyang Ekwo, ya umarci 'yan majalisa duk da kakaki, wanda ya bi bayan gwamna Umahi zuwa APC da su aje kujerun su.

Sunaye: Gwamnoni, 'yan majalisar tarayya da jiha da za su iya rasa kujerunsu kan sauya sheka
Sunaye: Gwamnoni, 'yan majalisar tarayya da jiha da za su iya rasa kujerunsu kan sauya sheka. Hotuna daga Femi Adesina
Asali: Facebook
"Kuri'u a kowanne zabe a Najeriya ta jam'iyya ce, saboda jam'iyya ake kada su, ba don 'yan takara," a cewar alkalin.

Alkali Ekwo yayi umarni da amsar dukkan albashi da alawus daga wadanda ake kara, daga lokacin da aka kwace kujerun su zuwa yanzu, gami da mika su ga asusan gwamnati.

Idan wannan hukuncin yayi tasiri, a kalla gwamnonin Najeriya guda biyu za su fuskanci irin wannan kaddarar.

Kara karanta wannan

Hisbah ta yi ram da zuka-zukan 'yan mata 2 suna shan wiwi da miyagun kwayoyi

Gwamnonin da suka sauya sheka

Kamar yadda ya faru a Ebonyi, PDP ta shigar da kara babban kotun tarayyar Abuja, inda ta bukaci kotu da ta kori Ayade, mataimakin shi da sauran wadanda suka sauya sheka zuwa APC.

A karar da tawagar lauyoyi karkashin jagorancin Emmanuel Ukala (SAN) ta shigar, PDP ta kalubalanci hakkin da ta bawa Cross River na zabe, inda ta nan ne Ayade yayi takara, ta kara da cewa hakkin ba zai yi amfani a Jam'iyyar APC ko wata jam'iyyar siyasa ba.

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara a watan Yuni, 2021, ya sauya sheka daga PDP zuwa APC.

Wasu fusattatun mambobin jam'iyyar PDP sun nufi kotu, inda suka bukaci sauke Matawalle daga madafun iko bisa sauya shekar da yayi.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Kotu ta ba gwamnan APC umarnin ci gaba da zamansa a ofis bayan umarnin tsige shi

Sai dai, a zaman da aka yi a kotun tarayya ta jihar Zamfara, a watan Fabrairu, tayi watsi da karar. Yayin zaman kotu a ranar Litinin, 7 ga watan Fabrairu, Alkali mai shari'a, Aminu Aliyu, ya ce, kotun ba ta da hurumin sauraran wannan karar.

Ya kara da cewa, kundin tsarin mulkin PDP da na gwannatin tarayyar Najeriya ba su haramta wa wani damar shiga wata kungiya ko jam'iyyar ba.

Aliyu ya ce, kotun sauraran kararrakin zabe ko 'yan majalisu ne ke da ikon tumbuke gwamna daga kujerar sa. Ba tare da kasa a guiwa ba, akwai wata kara da aka shigar a kotun koli da ba a yanke hukunci akan gwamna Matawalle ba.

'Yan majalisun jiha

'Yan majalisu guda biyu, Yekini Idaiye (mai wakiltar Akoko- Edo1) da Nosayaba Okunbor ( mai wakiltar gabacin Orhionmwon), da suka sauya sheka daga PDP zuwa APC a watan Fabrairu, 2021. Akwai yuwuwar zasu rasa kujerun su idan PDP ta kaisu kotu.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta maida zazzafan martani kan tsige gwamnan Ebonyi da ya sauya sheka daga PDP

A majalisar dattawa, yan majalisu da dama ( a majalisar dattawa da ta jiha) da yuwuwar tumbuke su daga madafun iko bisa sauya shekar da suka yi.

Majalisar dattawa

A majalisar dattawa, a kalla sanatoci shida sun sauya sheka daga PDP zuwa APC. Sune:

  1. Sanata Stella Oduah (mai wakiltar arewacin Anambra)
  2. Elisha Abbo ( Arewancin Adamawa)
  3. Peter Nwabaoshi (Arewancin Delta)
  4. Sahabu Ya'u ( Arewancin Zamfara)
  5. Lawali Anka ( Yammacin Zamfara)
  6. Emmanuel Bwacha (Tsakiyar Taraba)

Majalisun wakilai

Wasu 'yan majalisun jiha da suka sauya sheka daga PDP zuwa APC su hada da:

  1. Jonathan Gaza (Jihar Nasarawa)
  2. Ephreaim Nwuzi ( gundumar Etche/ Omuma, na jihar Rivers)
  3. David Abel ( gundumar Gashaka/Kurmi,Sardaunan jihar Taraba)
  4. Idagbo Ochiglegoor ( gundumar Obanliku)Obudu/Bekwarra ta jihar Cross River)
  5. Michael Etaba ( mazabar Obubra/Etung na jihar Cross River)
  6. Dan majalisa Bello Hassan Shinkafi ( jihar Zamfara)
  7. Ahmad Shehu (jihar Zamfara)
  8. Suleiman Gumi (jihar Zamfara)

Kara karanta wannan

Tsige gwamnan Ebonyi: Shehu Sani ya bayyana abun da zai faru da sauran gwamnonin da suka sauya sheka

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng