Babu wani aibu don mutum ya sauya sheka a siyasa - Kwankwaso
- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce bai ga wani aibu ba don dan siyasa ya sauya sheka zuwa wata jam’iyya
- Tsohon gwamnan na jihar Kano ya ce hakan wani salo ne na sanin farin jinin mutum da kuma sanin ko ya samu karbuwa a wajen mutane
- Ya kuma ce har yanzu yana PDP amma shirye-shirye sun yi nisa na sauya shekarsa zuwa jam’iyyar NNPP tunda rikici ya yi yawa a jam'iyyar tasa
Kano - Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa shi bai ga wani aibu ba don yan siyasa sun sauya sheka daga wata jam’iyya zuwa wata, cewa hakan wani tsari ne na siyasa.
Kwankwaso ya bayyana cewa akwai hikima sosai idan dan siyasa ya sauya sheka zuwa wata jam’iyya domin gwada farin jininsa da kuma karbuwarsa a cikin mutane.
Dan siyasan ya bayyana hakan ne a Kano, a ranar Lahadi, 6 ga watan Maris, yayin wata ganawa da yan Kwankwasiyya da kuma jiga-jigan PDP a jihar a gidansa da ke Miller Road, Daily Trust ta rahoto.
Ya ce:
“Tsayawa ko barin wata jam’iyya ba aibu bane a siyasa. A zahirin gaskiya, hakan na nuni ga cewar ka san ta kan siyasa sosai kuma za ka iya tafiya da dukka kalubalensa."
Ya tuna cewa a 2018 bayan babban taron shugaban kasa na PDP a Port Harcourt, hudu daga cikinsu da suka zo na daya, biyu, uku da hudu duk sun bar jam’iyyar sannan daga baya suka dawo PDP.
Kwankwaso ya kara da cewar koda dai har yanzu yana PDP, zai bar jam’iyyar nan ba da dadewa ba zuwa jam’iyyar New Nigeria Progressive Party (NNPP) tunda jam’iyyarsa ta yanzu ita ma tana fuskantar gagarumin rikici mai wuyan sha’ani, rahoton Aminiya.
Kwankwaso ya kuma ce:
“Koda dai APC ce jam’iyyar da ta fi bayar da kunya a Najeriya, kusan suna a sahu daya da PDP, tunda ita ce jam’iyyar da ake wofantar da yancin mutum.
“Duk yadda ka kai ga nagarta sai an samu wadanda za su yi kokarin kai ka kasa.”
Kafin karshen watan nan zan fita daga jam'iyyar PDP, Rabiu Musa Kwankwaso
A baya mun ji cewa jagoran darikar Kwankwasiyya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa kafin karshen watan nan zai fice daga jam'iyyar hamayya ta Peoples Democratic Party PDP.
BBC Hausa ta ce tsohon gwamnan ya bayyana mata hakan.
Har ila yau Kwankwaso ya tabbatar da labarin cewa ya yi nisa a shirinsa na komawa jam'iyyar NNPP watau New Nigeria Peoples Party.
Asali: Legit.ng