Rikicin APC a Zamfara: Magoya Bayan Matawalle a Garinsu Sun Juya Masa Baya, Sun Koma Ɓangaren Marafa
- ‘Yan jam’iyyar APC na karamar hukumar Maradun da ke Jihar Zamfara, asalin garin su gwamna Bello Matawalle sun bayyana goyon bayan su ga bangaren Sanata Kabiru Garba Marafa na jam’iyyar
- Captain Halilu Halliru mai murabus da tsohon darekta janar na ma’aikatan gwamnati, Malam Sale ST ne suka yi wa ‘yan jam’iyyar jagora wurin yi wa Matawalle tawaye
- Sun bayyana dalilan su na barin bangaren Matawalle inda suka ce ba ya tabuka wani aikin a zo a gani a jihar, kuma Hon. Bello Bakyasuwa, jagora a bangaren Sanata Marafa ne ya amshe su
Zamfara - Jiga-jigan jam’iyyar APC daga karamar hukumar Maradun, asalin garinsu Gwamna Bello Matawalle, sun bayyana goyon bayan su ga bangaren jam’iyyar na Sanata Kabiru Garba Marafa, The Punch ta ruwaito.
Muhammad Hassan Nasiha: Abubuwa 5 Da Ya Kamata Ka Sani Game Da Sabon Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara
Jagororin su sun hada da Captain Halilu Haliru mai murabus da kuma tsohon darekta janar na ma’aikatan gwamnatin jihar, Malam Sale ST, wadanda suka yanke shawarar juya wa Matawalle baya akan gaza yi wa jihar aikin a zo a gani.
Bangaren da suka juya masa baya sun samu karbuwa zuwa bangaren APC na Sanata Marafa, inda Hon Bello Bakyasuwa ya amshe su hannu bibbiyu.
Daga Bakyasuwa har Matawalle daga karamar hukuma daya suke
Bakyasuwa ma dan asalin karamar hukumar su Matawalle ne kuma yanzu haka shi ne sakataren watsa labarai na APC ta bangaren Sanata Marafa kamar yadda The Punch ta nuna.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya amshe su a maimakon shugaban bangaren Sanata Marafa, Alhaji Sirajo Maikatako, a ofishin su da ke Gusau, bayan shirya gagarumin biki.
Yayin jawabi a taron, shugaban kungiyar, Captain Halilu ya ce abinda ya ja hankalin su shi ne gaskiya da aikin Marafa, wanda suka kwatanta a matsayin kishiyar tsohon shugaban su, Matawalle.
Ya ce Matawalle ba jagora na kwarai bane don haka suka yanke shawarar mara wa Marafa baya don kawo ingantaccen shugabanci a jihar.
Captain Halilu ya ce Matawalle ba jagoran kwarai bane
Captain Halilu ya kara da cewa:
“Mun san kokarin da Marafa ya yi wurin kawo ci gaba ga mazabar sa a matsayin sa na Sanatan gwamnatin tarayya.
“Yanayin ayyukan sa da ya yi wa jiharsa musamman a farko-farkon rashin tsaron da ya addabi jihar da kuma ayyukan da ya samar wa dubannin jama’a sun nuna cewa shi jajirtacce ne.”
Ya bayyana yadda Matawalle yayi dare-dare akan madafun iko na tsawon lokaci ba tare da ya yi wani aiki ba.
A cewarsa, babu wani abin nunawa da Matawalle ya yi a garin Maradun.
A bangaren Honarabul Bello Bakyasuwa kuwa ya nuna jin dadin sa akan yadda jiga-jigan APC na Maradun suka koma tafiyar su, kuma ya tabbatar musu da jajircewar Marafa wurin ganin ya ci gaba da aiki na kwarai a jihar wanda zai kawo ci gaba.
2023: Manya masu son satar dukiyar talakawa ne ba su son a sake samun wani Buharin, Garba Shehu
A wani labarin daban, Fadar Shugaban Kasa ta ce manyan mutane masu aikata rashawa ne ba su son a sake samun 'wani Buhari' a Najeriya saboda wata manufarsu na gina kansu, Daily Trust ta ruwaito.
Mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari, Garba Shehu, cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya ce zai yi wahala a samu wani shugaba da zai iya zarce irin ayyukan da Buhari ya yi.
Ya yi bayanin kan dalilin da yasa Buhari ba zai 'bari a cigaba da yadda ake harka' a kasar ba a karkashin gwamnatinsa.
Asali: Legit.ng