2023: Ministan Buhari Ya Ce Yana Shawara Domin Fitowa Takarar Kujerar Shugaban Kasa
- A ranar Alhamis ministan kwadago da ayyuka, Chris Ngige ya ce yanzu haka ya zage damtsensa wurin tsayawa takarar shugaban kasa a 2023
- Ya bayyana wannan kudirin nashi ne a wata tattaunawa da Channels TV ta yi da shi a wani shiri na siyasa inda yace yanzu haka ya fara kamfen
- Ministan ya ce yana da duk wasu halayen da suka dace shugaban kasa ya mallaka duk da dai har yanzu bai bayyana wa shugaba Buhari kudirinsa ba
Ministan kwadago da ayyuka, Chris Ngige ya bayyana shirin sa na tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2023 a ranar Alhamis.
Ya bayyana wannan shirin nasa yayin da yayin da Channels TV take tattaunawa da shi a wani shiri na siyasa a yau.
Kamar yadda ya shaida:
“Na sanar da mutane na wadanda suka matsa min a watan Disamban da ya gabata cewa zan fara tuntubar jama’a. Kuma zan yi musu magana a watan Afirilu, lokacin Easter. Don haka yanzu haka ma na fara kamfen.”
Ministan ya ce wasu ne suka bukaci ya tsaya takara
Ministan ya kara da cewa yana da duk halayen da suka dace a zabi shugaban kasa da su amma bai riga ya sanar da shugaba Muhammadu Buhari ba.
Kamar yadda ya ce, wasu ‘yan Najeriya, ciki har da tsohon sifeta janar na ‘yan sanda ne suka bukaci ya tsaya takara, rahoton Channels TV.
Yayin da ake tsaka da batun kawo shugaban kasa daga yankin kudu maso gabas, Ngige ya ce ba saboda yanki yake son ya tsaya takara ba.
Ya ce ya cancanci zama shugaban kasa
Ngige ya ce:
“Ba don ni Igbo bane yasa nake so in tsaya takara ba. Zan tsaya takara a matsayina na Chris Nwabueze Ngige, dan Najeriya, daga yankin kudu maso gabas kuma dan Jihar Anambra daga karamar hukumar Idemilli ta kudu, dan wani gari mai suna Alor.
“Ni dan kabilar Igbo ne amma ina da duk halayen da shugaban kasar Najeriya ya dace ya mallaka.”
2023: Ƙungiyar musulmai ta buƙaci Gwamna Ugwuanyi ya fito ya nemi kujerar Buhari
A wani rahoton, kungiyar hadin kan al’ummar musulmi, UMUL ta bukaci dan kabilar Ibo ya tsaya takarar shugaban kasa idan 2023 ta zo, The Sun ta ruwaito.
Kungiyar ta musulmai ta ce lokaci ya yi da cikin yankuna biyar da ke kasar nan, ko wanne yanki zai samu adalci da daidaito da juna, hakan yasa take goyon bayan Igbo ya amshi mulkin Najeriya.
Kamar yadda kungiyar ta shaida, dama akwai manyan yaruka uku a Najeriya, Hausa, Yoruba da Ibo, don haka in har ana son adalci, ya kamata a ba Ibo damar mulkar kasa don kwantar da tarzomar da ke tasowa.
Asali: Legit.ng