2023: Dattawan Arewa Sunyi Taro, Sun Yanke Shawarar Goyon Bayan Igbo Ya Maye Gurbin Buhari

2023: Dattawan Arewa Sunyi Taro, Sun Yanke Shawarar Goyon Bayan Igbo Ya Maye Gurbin Buhari

Kaduna - Kungiyar Dattawan Arewa ta Forum of Northern Elders for Unity (FNEU) ta yanke shawarar za ta goyi bayan Gwamna Uguwanyi a matsayin dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP a shekarar 2023, rahoton Vanguard.

Kungiyar ta bada dalilanta na yin hakan inda ta ce da farko, gwamnatin PDP ta janyo kowa jiki a lokacin mulkinta ta hada kan Najeriya sai kuma ta ce ba adalci bane shekaru 22 bayan komawa demokradiyya kudu bata samu shugaban kasa ko mataimaki ba.

2023: Dattawan Arewa Sunyi Taro, Sun Yanke Shawarar Goyon Bayan Igbo Ya Maye Gurbin Buhari
2023: Dattawan Arewa Sun Yanke Shawarar Goyon Bayan Igbo Ya Gaji Buhari. Hoto: Vanguard
Asali: Twitter

Dattawan sun ce:

"Daya cikin dalilan yin taron mu a yau shine samar da dandali na tuntuba da zai taimaka kwantar da hankula sakamakon farfagandan da wasu yan siyasa masu son kai suke yada wa na lalata Najeriya da muka yi wahalar gina wa," in ji dattawan.

Kara karanta wannan

Rikicin Masarautar Kano da Kamfanin jirgi: Ya kamata manya su saka baki, inji wata kungiya

A cikin sakon bayan taro da ta fitar, a ranar Litinin a Kaduna, Kungiya Dattawa ta hadin kai ta ce jam'iyyar APC mai mulki yanzu tana da shugaba dan arewa, don haka zai dace ta bawa kudu, musamman Igbo takara na gaba saboda ware su da aka yi a siyasance.

Shugaban kungiyar, Alhaji Bala Mala da Sakatarenta, Mal Yau Aliyu ne suka saka hannu kan sanarwar bayan taron, inda suka bukaci PDP ta tsayar da Gwamna Ifeani Ugwuanyi saboda kasancewarsa shugaba mai son zaman lafiya, hadin kai da cigaban kasa.

Wani sashi na sakon ya ce:

"Mun yi nazarin dukkan gwamnonin kudu maso gabas mun gano Gwamna Uguwanyi mutum ne mai hangen nesa da za mu iya amincewa da shi a mulki."
"Kuma idan PDP tana son ta ci zaben shugaban kasa na 2023, ta duba yiwuwar bawa Gwamna Ugwuanyi tikiti kuma a shirye muke mu yi aiki don ganin ya yi nasara a zabe.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Wata kungiyar arewa ta goyi bayan Jonathan ya tsaya takara

"Mun fito ne daga yankin kasa mai dimbin mutane don haka mu za mu iya zaben wanda zai zama shugaban kasa, don haka za mu cigaba da aiki don kwantar da hankula da suka tashi saboda batun mulki."

Kungiyar ta kuma yi kira ga Igbo da yan kudu su hada hannu da NEFU su roki yan Najeriya daga sauran yankuna su goyi bayan tsarinsu na kasa daya tare da dan takarar shugaban kasa wanda ya fi dacewa.

Saurari karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164