Dan takarar PDP ya lashe zaben cike gurbi na Jos ta arewa
- Jam'iyyar PDP mai adawa ta lashe zaben cike gurbi na dan majalisar tarayya mai wakiltan Jos ta Arewa/Bassa
- Hukumar zabe mai zaman kanta ta bayyana dan takarar jam'iyyar Hon. Musa Agah a matsayin wanda ya yi nasara bayan ya samu kuri'u 37, 757
- INEC ta sanar da sakamakon ne a ranar Lahadi, 27 ga watan Fabrairu
Plateau - Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC), ta ayyana Hon. Musa Agah na jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) a matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbi na dan majalisar tarayya mai wakiltan Jos ta Arewa/Bassa.
INEC ta bayyana hakan ne a ranar Lahadi, 27 ga watan Fabrairu, jaridar The Nation ta rahoto.
Baturen zabe, Dr Oyeyinka Oyerinda, ya sanar da cewar Agah ya samu kuri’u 40, 343 wajen kayar da dan takarar jam’iyyar PRP, Hon. Muhammad Gwani, wanda ya samu kuri’u 37, 757, Daily Post ta rahoto.
Hon. Abbey Aku na jam’iyyar All Progresives Congress (APC) mai mulki ya samu kuri’u 26,111.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sanata Istifanus Gyang ya yi martani ga nasarar da PDP ta samu
Sanata Istifanus Gyang na Plateau ta arewa ya taya Agah murnar nasarar da ya yi.
Sanatan a cikin wani jawabi daga kakakinsa, Muas Ashoms, ya ce kayen da APC ta sha hukunci ne kan kiyayyar zabe da Gwamna Simon Lalong ya yi na zaben wanda ya sa PLASIEC ta ki amincewa PDP shiga zaben karamar hukuma a jihar.
Ya ce nasarar alamu ne na abubuwa masu kyau da ke zuwa.
Hukumar INEC ta sanar da ranar zaben shugaban kasa na 2023
A wani labarin, hukumar shirya zabe ta kasa mai zaman kanta INEC ta sanar da ranar da za'a gudanar da zaben shugaban kasa, yan majalisa da gwamnoni na shekarar 2023.
Shugaban hukumar, Farfesa Mahmoud Yakubu, ya sanar da hakan a hira da manema labarai ranar Asabar a birnin tarayya Abuja.
A cewarsa, za'a gudanar da zaben Shugaban kasa da na majalisar dokokin tarayya ranar Asabar, 25 ga watan Febrairu, 2023.
Asali: Legit.ng