Kwankwaso, tsohon ministan Buhari: Jerin yan siyasar da suka kafa sabuwar kungiyar siyasa
Abuja – Gabannin babban zaben 2023, an kafa wata sabuwar kungiyar siyasa da ke neman karbe mulki daga hannun jam’iyyun All Progressives Congress (APC) da Peoples Democratic Party (PDP).
Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso ne ya sanar da kafa sabuwar kungiyar siyasar mai suna ‘The National Movement (TNM)’ a babban cibiyar taro ta kasa da ke Abuja, a ranar Talata, 22 ga watan Fabrairu.
Ga jerin yan siyasar da suka halarci taron kaddamar da sabuwar kungiyar:
1. Rabiu Kwankwaso
Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso, ya kasance jigon jam'iyyar PDP har zuwa lokacin da ya sanar da kafa sabuwar kungiyar.
A jawabansa na baya ya bayyana cewa APC da PDP basu da wani abun nunawa yan Najeriya a 2023.
Kwankwaso ya sha yunkurin zama shugaban kasa amma bai cimma nasara ba.
2. Sanata Suleiman Hunkuyi
Sanata Suleiman Hunkuyi ya wakilci Kaduna ta arewa a majalisar dokokin tarayya ta takwas. Ya bar APC zuwa PDP gabannin zaben 2019.
Ya yi takarar tikitin gwamna na jam'iyyar PDP amma ya sha kaye a hannun Isa Ashiru.
3. Solomon Dalung
Solomon Dalung ya rike mukamin ministan matasa da wasanni a karkashin gwamnatin Muhammadu Buhari ta farko.
Yana daya daga cikin ministocin da basu samu damar komawa majalisar Buhari ta biyu ba bayan sake zabarsa.
4. Buba Galadima
Buba Galadima ya kasance na hannun damar shugaba Buhari kafin alakarsu ta yi tsami gabannin zaben 2019.
5. Idris Wada
Idris Wada ya kuma kasance jigon PDP sannan tsohon gwamnan jihar Kogi.
Sauran manyan yan Najeriya da suka hallara a wajen sanar da sabuwar kungiyar sune:
6. Tanko Yakasai
7. Air Vice Marshall Ifeanaju
8. Solomon Edoda
9. Nweze Onu
10. Falasade Aliyu
11. Rufai Alkali
12. Grace Ben
13. Umale Shittu
14. Ibrahim Ringim
15. Ali Gwaska
16. Paul Okala
17. Rufai Hanga
18. Abdulrahman Abubakar, da sauransu.
Duk da sun kafa TMN, Kwankwaso ya na nan daram-dam-dam a jam’iyyar PDP
A gefe guda, mun ji cewa Rabiu Musa Kwankwaso wanda shi ne jagoran sabuwar tafiyar siyasa ta The National Movement a Najeriya, ya yi karin haske kan inda suka sa gaba.
Sanata Rabiu Kwankwaso a wata hira da ya yi da BBC Hausa, ya tabbatar da cewa bai sauya-sheka daga jam’iyya PDP kamar yadda wasu mutane ke tunani ba.
Kwankwaso ya ce The National Movement kungiya ce ba jam’iyyar siyasa ba, wanda suka kafa domin ganin an fitar da Najeriya daga halin da take ciki a yanzu.
Asali: Legit.ng