Fani-Kayode: 'Yan siyasa suna shirin tarwatsa APC da PDP, za su kafa tasu jam'iyyar
- Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya ce akwai 'yan siyasa da suka shirya tarwatsa manyan jam'iyyun kasar nan
- Fani-Kayode ya ce 'yan siyasan sun shirya tsaf bayan tarwatsa jam'iyyun PDP da APC sannan su kafa tasu jam'iyyar kafin 2023
- Dan siyasan ya ce bai dace a dinga sukar Buni ba kan shugabancin jam'iyyar ganin irin nagartar da ya ke da ita
Femi Fani-Kayode, tsohon ministan sufurin jiragen sama ya ce wasu 'yan siyasa suna kokarin ganin sun tarwatsa jam'iyyun All Progressives Congress (APC) da Peoples Democratic Party (PDP) domin su kafa wata a zaben 2023.
Fani-Kayode ya sanar da hakan ne a ranar Litinin yayin tattaunawa da ChannelsTV.
A yayin da watanni kadan suka rage zuwa zaben 2023, ana ta samun rikicin cikin gida a manyan jam'iyyun kasar nan na PDP da APC.
A wani hukuncin jam'iyyar APC, wasu 'ya'yan jam'iyyar sun zargi kwamitin shugabancin jam'iyyar karkashin Mai Mala Buni da katantane tsarin shugabancin jam'iyyar ta hanyar jinkirta gangamin zaben shugabannin jam'iyyar na kasa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sai dai kuma a ranar Litinin, jam'iyyar ta sanar da cewa ta saka gangamin zaben shugabannin jam'iyyar zuwa ranar 26 ga watan Maris a maimakon ranar 26 ga watan Fabrairu.
A yayin tsokaci a kan Buni, tsohon ministan ya ce bai dace a dinga caccakar gwamnan jihar Yoben ba kan zaben shugabannin jam'iyyar ba tare da duban kalubalen da jam'iyyar ke fuskanta ba, TheCable ta ruwaito.
Fani-Kayode ya bayyana cewa akwai wadanda suka yi kokarin hana shi sauya sheka, amma ganin yadda Buni ke fafutuka, hakan yasa ya janyo jama'a masu yawa.
“Dole ne a gode masa sakamakon kalubalen da ya ke fuskanta, Kalubalen farko shi ne yadda wasu 'yan siyasa suke kokarin kwace zaben shugabancin jam'iyyar tare da manna 'yan takararsu.
“Akwai wasu a jam'iyyar da ke son zama shugabannin kasa kuma sun shirya tsaf domin assasa zaben ta hanyar yin amfani da kudin da suke da shi wurin kakaba 'yan takararsu ta yadda 2023 za ta zama musu da sauki.
“Idan kuma ka duba PDP, akwai wasu da ke kokarin ganin sun kafa jam'iyyarsu. Wadannan suna daga cikin matsalolin da ya dace jama'a su duba," yace.
Fani-Kayode: Abin da ya sa aka ji ni a APC duk da na yi wa Shugaba Buhari da wasu ta-tas a baya
A wani labari na daban, tsohon Minisan harkokin jirgin sama, Femi Fani-Kayode, ya kare kan shi na koma wa APC bayan tsawon shekaru yana caccakar jagororinta.
Cif Femi Fani-Kayode yayi magana a gidan talabijin na Channels TV, inda ya yi karin haske a kan dalilin koma warsa jam’iyyar APC mai mulki daga PDP.
Da yake magana a shirin ‘Politics Today’, Cif Fani-Kayode yace ya rika sukar Muhammadu Buhari ne saboda a lokacin ya jahilci wanene shugaban kasar.
“Na rika magana game da Buhari ne daga waje, yanzu na san shi ciki-da-bai. Ba cewa nake yi mutumin kirki ba ne shi ko na banza.”
Asali: Legit.ng