An tsaurara tsaro: Majalisar jiha na shirin tsige mataimakin kakaki bisa kin jinin APC

An tsaurara tsaro: Majalisar jiha na shirin tsige mataimakin kakaki bisa kin jinin APC

  • Rahotannin da muke samu daga jihar Ebonyi sun bayyana cewa, majalisar dokokin jihar na kitsa yadda za ta tsige mataimakin kakakin majalisa
  • Wannan na zuwa ne bayan da mataimakin kakakin ya ki amince da komawa jam'iyyar APC mai mulkin jihar
  • An tsaurara tsaro a majalisar, inda ake sa ran zaman zai kai ga tsige mataimakin kakakin majalisar daga mukaminsa

Jihar EbonyiAn tsaurara matakan tsaro a majalisar dokokin jihar Ebonyi yayin da majalisar ke shirin zama a yau Litinin 21 ga watan Fabrairu.

Lamarin ya kara dagula rade-radin da ke cewa majalisar na shirin tsige mataimakin kakakin majalisar, Odefa Obasi Odefa.

Odefa ya bayyana zargin tsige shi ne a ranar Asabar, inda yace majalisar na shirin tsige shi daga kujerarsa ba bisa ka’ida ba.

Ana shirin tsige mataimakin kakakin majalisar wata jiha
Gudun tada zaune tsaye: An girke jami'an tsaro yayin da ake kokarin tsige mataimakin kakakin majalisar jiha | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Ya yi zargin cewa shirin ya biyo bayan matakin da ya dauka na kin sauya sheka zuwa APC.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Sojin Najeriya sun ragargaji 'yan ISWAP da Boko Haram a Adamawa

Odefa, dan majalisar da ke kan wa’adi na hudu, wanda ke wakiltar mazabar Onicha ta Gabas, an zabe shi ne a karkashin jam’iyyar PDP.

A lokacin gabatar da wannan rahoto, kamar yadda The Nation ta ruwaito, ‘yan majalisar da aka ce suna biyayya ga gwamnatin APC a jihar sun hallara domin shirin zaman majalisa.

Wata majiya ta ce shugabannin majalisar sun tattara sa hannun ‘yan majalisa sama da 15 domin tsige mataimakin kakakin.

Zamfara: Ba Umarnin Kotun da zai hana mu tsige mataimakin gwamna, Majalisa

Majalisar dokokin jihar Zamfara, a ranar Talata, ta ce babu wani umarnin kotu da zai dakatar da ita daga tsige mataimakin gwamna, Mahdi Aliyu Gusau.

Daily Trust ta rahoto cewa shugaban kwamitin bayanai, Alhaji Shamsuddeen Bosko, shi ne ya faɗi matsayar majalisar a wani taron manema labarai a Gusau.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Saraki ya cancanci darewa kujerar Buhari, in ji kungiyar matasa

Bosko ya yi bayanin cewa shirin tsige mataimakin gwamnan ya yi dai-dai da dokar sashi na 188 (5) (7) a kundun dokokin mulkin tarayyan Najeriya.

Bisa haka, a cewarsa, "Babu wani umarnin Kotu da zai dakatar da majalisar dokokin Zamfara daga tsige mataimakin gwamnan."

Honorabul Bosko ya ƙara da cewa a halin yanzun yan majalisu 18 daga cikin 24 sun kaɗa kuri'ar amincewa da shirin a zaman majalisar, kamar yadda Tribune ta rahoto.

Rana ba ta karya: An sa sabon ranar shari’a da ‘Dan Majalisar da ake zargi da takardun ‘bogi’

A wani labarin, hukumar ICPC mai binciken masu laifuffuka a Najeriya ta na tuhumar Mohammed Garba Gololo da laifin amfani da takardun digiri na bogi.

Jaridar The Nation ta fitar da rahoto a ranar Litinin, 21 ga watan Fubrairu 2022 cewa an shigar da karar Honarabul Mohammed Garba Gololo a kotu.

An maka Mohammed Gololo mai wakiltar mazabar Gamawa a jihar Bauchi a majalisar wakilai ne a babban kotun tarayya da ke zama a garin Abuja.

Kara karanta wannan

Kusoshin Gwamnati za su amsa tambayoyi a Majalisa kan zargin cuwa-cuwar albashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.