Siyasar Kano: Ganduje ya yi wa Shekarau sabon shagube, ya yabawa aikin Kwankwaso
- Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya yabi abokin gabansa a siyasa, Rabiu Kwankwaso
- Dr. Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa shi da Sanata Kwankwaso ne suka gyara jihar Kano a zamanin nan
- Da alama Gwamnan ya yi haka ne domin ya tsokani Shekarau ko kokarin shawo kan Kwankwaso
Kano – A karshen makon jiya Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya fito, ya na yabon gwamnatin tsohon mai gidansa, Rabiu Musa Kwankwaso.
A wajen wani taro na jam’iyyar APC mai mulki da aka yi a gidan gwamnatin Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya yabawa gwamnatinsa da ta ubangidansa.
Kamar yadda Legit.ng Hausa ta ji a wani bidiyo a shafin Facebook, Mai girma Abdullahi Ganduje ya ce shi da Rabiu Kwankwaso suka canza fasalin jihar Kano.
A shekarun da aka yi a mulkin farar hula a jihar Kano, Gwamna mai-ci ya ce shi da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso suka kawo ayyukan da ake gani a yau.
Zuwan wani Bafullatani
Gwamnan ya fake da labarin wani Bafullatani wanda ya ce ya zo Kano bayan tsawon shekaru 15 ba ya nan, sai ya ga jihar ta rikide masa, ba yadda ya santa ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewar Ganduje, da wannan mutumi ya yi tambaya, sai aka shaida masa cewa wannan sabuwar Kano ce da wanda gwamna Ganduje da Kwankwaso suka gina.
Ina aka baro Shekarau?
Duk da cewa Malam Ibrahim Shekarau ya yi mulki daga shekarar 2003 zuwa 2011, Gwamna Ganduje bai ambace shi a wadanda suka yi abin a-yaba ba.
Shekarau shi ne gwamnan farko da ya fara yin tazarce a jihar Kano. Ana tunanin rikicinsu na cikin gida ne ya hana gwamna Ganduje ya yaba da ayyukansa.
Sanata Shekarau yana cikin bangaren ‘yan taware a jam’iyyar APC mai mulki. A gefe gudu kuwa an raba jiha tsakanin Ganduje da Kwankwaso tun kafin 2018.
Aika-aikar Kwankwaso
A farkon mulkinsa, an taba jin Abdullahi Ganduje yana caccakar Sanata Rabiu Kwankwaso, inda yace gwamnatinsa ta yi aiki, sannan tayi tulin aika-aika a baya.
A wancan lokaci, hakan ya ba mutane mamaki ganin cewa Kwankwaso ya yi shekaru takwas yana mulki ne da Ganduje a matsayin mataimakinsa tun daga 1999.
Kwankwaso zai bar PDP?
Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kira taro na musamman, amma ba a ga jagororin tafiyarsa PDP da Kwankwasiyya a wajen zaman ba.
Hakan ya biyo bayan an ji Muaz Magaji ya ce irinsu Yunusa Dangwani, Madakin-Gini, Yusuf Danbatta za su dawo APC domin taya su yakar Abdullahi Ganduje.
Asali: Legit.ng