Da Dumi-Dumi: Tsagin Sanata Shekarau zai daukaka kara kan Nasarar Ganduje a Kotu

Da Dumi-Dumi: Tsagin Sanata Shekarau zai daukaka kara kan Nasarar Ganduje a Kotu

  • Bangaren APC a jihar Kano wanda Shekarau ke jagoranta yace zai yi wa Kotu biyayya amma zai ɗaukaka kara zuwa gaba
  • A ranar Alhamis da muke ciki, Kotun daukaka kara ta jingine hukuncin babbar Kotun tarayya, ta ce bangaren Ganduje ne halastacce
  • A halin yanzu matukar suka sake ɗaukaka kara, hakan na nufin Kotun Koli ta Allah ya isa ce zata raba wa ɓangarorin gardama

Kano- Tsagin jam'iyyar APC wanda Sanata Ibrahim Shekarau ke jagoranta a jihar Kano, yace zai ɗaukaka kara kan hukuncin da ya baiwa ɓangaren Ganduje nasara.

Shugaban APC na tsagin, Malam Ahmadu Haruna Zago, ya shaida wa BBC Hausa cewa ɓangaren su zai wa kotu biyayya amma za su ɗauki matakin ɗaukaka kara zuwa gaba.

Rikicin APC a Kano
Da Dumi-Dumi: Tsagin Sanata Shekarau zai daukaka kara kan Nasarar Ganduje a Kotu Hoto: punchng.com
Asali: UGC

A kalamansa, Haruna Zago, mai goyon bayan tsohon gwamna Malam Shekarau, ya ce:

Kara karanta wannan

Karin bayani: Tsohon mashawarcin Tinubu lokacin da yake gwamna ya rasu

"Zamu ɗaukaka kara zuwa gaba kan hukuncin domin bin umarnin da Kotu ta bayar daban kuma ɗaukaka kara shi ma daban."
"A halin yanzu Lauyoyin mu na nazarai kan hukuncin da Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke."

A halin yanzun Kotun ɗaukaka kara ce ta yanke hukunci tsakanin ɓangarorin biyu, matukar tsagin Shekarau zai ɗaukaka ƙara to Kotun Koli ce zata raba gardama.

Bangaren Ganduje ya yi nasara a Kotu

Bangaren jam'iyyar APC dake goyon bayan gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Ganduje ya samu nasara a karon farko a Kotu.

A zaman Kotun ɗaukaka ƙara na yau Alhamis, Kotun ta ce babbar Kotun tarayya dake zamanta a Abuja ba ta da ikon yanke hukunci kan lamarin.

Kazalika Kotun ta ce shugabannin APC da aka zaɓa na tsagin gwamna Umar Ganduje ne sahihan shugabannin jam'iyya a Kano.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Duk a babi daya muke, Dattawan Arewa sun gana da Obasanjo

Idan baku manta ba, Ɓangaren Shekarau a makon da ya shuɗe, ya yi watsi da matakin sulhun da uwar jam'iyya ta ƙasa ta yi tsakaninsu, inda ta naɗa Ganduje a matsayin jagora.

A wani labarin na daban kuma Manyan jiga-jigan APC da Mambobi sama da 5,000 sun sauya sheƙa zuwa PDP a jiha daya

Yayin da jam'iyyun siyasa ke shirin zaben 2023 dake tafe, Jam'iyyar PDP ta yi manyan kamu a jihar Bayelsa ranar Talata.

Wasu jiga-jigan jam'iyyar APC da kuma dubbannin mambobin jam'iyyar sun sauya sheka zuwa PDP a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262