2023: Atiku Ya Magantu Game Da Batun Karɓa-Karɓa a Mulkin Najeriya

2023: Atiku Ya Magantu Game Da Batun Karɓa-Karɓa a Mulkin Najeriya

  • Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, ya ce a cikin kundin tsarin mulkin Najeriya, babu inda ya nuna tsarin karba-karba a ko wanne matsayi na siyasa
  • Jigon na jam’iyyar PDP ya yi wannan furucin ne a wani taro da kungiyar ta da ke kira gare shi don ya tsaya takarar shugaban kasar Najeriya a shekarar 2023
  • Har yanzu dai Atiku bai bayyana kudirinsa na shiga jerin ‘yan takarar shugaban kasa ba, amma ya ce kalubalen da ke kasar nan ya na sa shi kokwanto idan zai iya tsayawa takara ko kuma ya fasa

Alhaji Atiku Abubakar, tsohon shugaban kasar Najeriya, ya ce a cikin kundin tsarin mulkin Najeriya babu wani tsari na karba-karba a ko wacce kujera, The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Jonathan Ya Goyi Bayan Gwamnan PDP Ya Zama Shugaban Ƙasa a 2023

Jigon na jam’iyyar PDP ya yi wannan bayanin ne a wani taro wanda ya yi da kungiyar da ke kira a gare shi don ya tsaya takarar shugaban kasa a 2023.

Atiku: Babu Tsarin Karɓa-Karɓa a Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, Kowa Zai Iya Takara a 2023
2023: Babu Karɓa-Karɓa a Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, Kowa Zai Iya Takara a 2023, Atiku. Hoto: Atiku Abubakar
Asali: UGC

Kawo yanzu, Atiku bai riga ya bayyana kudirinsa na tsayawa takara ba, amma ya ce wani lokacin idan ya kalli kalubalen da kasar nan take fuskanta ya kan sake tunani akan ya tsaya takara ko ya fasa tsayawa.

Atiku ya ce wani lokacin matashi zai iya mulkin da tsoho bai iya ba

A cewarsa:

“Shugabanci na Allah ne. Zaka iya ganin matashi mai karancin shekaru ya mulki kasa fiye da tsoho.
“Don haka komai na Ubangiji ne, mu yi kokarin neman wanda ya tara duk halaye na kwarai don mu ba shi shugabanci.

Kara karanta wannan

2023: Magoya bayan Atiku sun buƙaci ya haƙura da takara, ya goyi bayan ɗan takara daga kudu

“Ban taba ganin lokacin da kalubale ya yi yawa a kasar nan ba kamar yanzu. Wani lokacin ina kwance a gado na ina kokwanto idan zan yi takara. A rayuwa ta ban taba ganin Najeriya a wannan halin ba.”

A cewarsa kamar yadda The Cable ta ruwaito, a wannan halin talaucin da Najeriya take ciki har manomi ba ya iya zuwa gona balle ya samu abinci.

Ya ce babu inda aka kira batun tsarin karba-karba a kudin tsarin mulkin Najeriya

Dangane da karba-karba, Atiku ya ce a kundin tsarin mulkin Najeriya babu inda aka haramta wa wani yanki takarar shugaban kasa.

Ya ce babu wanda ba zai iya takara ba kuma babu wani batun karba-karba a yankunan Najeriya.

Ya bayyana yadda ‘yan majalisar tarayya suka duba kundin tsarin mulkin Najeriya ba su ga wani batu na tsarin karba-karba ba.

Jonathan Ya Goyi Bayan Gwamnan PDP Ya Zama Shugaban Ƙasa a 2023

Kara karanta wannan

Ku nemi kujerun sanatoci, ku bar matasa su shugabanci kasar - Tsohon ministan Buhari ga Atiku da Tinubu

A wani labarin, tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan ya bayyana yakinin sa akan Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi dangane da mulkin kasar nan a 2023, Channels TV ta ruwaito.

Kamar yadda aka samu rahoton, Jonathan ya yi wannan bayanin ne a ranar Alhamis, 10 ga watan Fabrairu yayin wani taro, inda yace ya san yadda gwamnan yake jajircewa akan yi wa kasa aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164