APC: Zan goyi bayan a zabi zaƙaƙuran matasa a manyan kujeru, Shugaba Buhari

APC: Zan goyi bayan a zabi zaƙaƙuran matasa a manyan kujeru, Shugaba Buhari

  • Shugaban ƙasa ya sha alwashin mara wa matasa masu kaifin basira baya su ɗare manyan kujeru a babban taron APC dake tafe
  • Buhari ya umarci shugaban ma'aikatan fadarsa da sakataren gwamnati su tabbatar an saka matasa a wasu wurare na gwamnatinsa
  • Shugaban ƙasa Buhari ya yi wannan furucin ne yayin da kungiyar haɗin kan matasan APC suka kai masa ziyara fadarsa yau Jumu'a

Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, rana Jumu'a, ya tabbatar wa matasan APC cewa zai goyi bayan zakakurai daga cikinsu su ɗare manyan muƙamai a taron APC dake tafe.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Buhari ya sha alwashin marawa matasan baya su samu mukamai a shugabancin APC na ƙasa a taron 26 ga watan Fabrairu, 2022.

Shugaba Buhari da matasa
APC: Zan goyi bayan a zabi zaƙaƙuran matasa a manyan kujeru, Shugaba Buhari Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Kazalika Buhari ya umarci shugaban ma'aikatan fadar gwamnati, Farfesa Ibrahim Gambari, da Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, su tabbatar an saka matasa masu hazaka a gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

Borno: Gwamna Zulum ya yi magana kan takarar shugaban ƙasa karkashin APC a 2023

Shugaban ya bukaci CoS da SGF su sanya matasa a hukumomin gwamnatin tarayya da har yanzun ba'a naɗa ba.

Bayan haka Shugaba Buhari ya roki matasan APC su yi aiki tukuru wajen tabbatar da jam'iyya ta cigaba da rike kujerun gwamnonin jihar Ekiti da Osun da zaɓen su ke tafe cikin 2022.

Buhari ya yi wannan jawabin ne yayin da ya karbi bakuncin mambobin kungiyar haɗa kan matasan jam'iyyar APC a fadarsa Aso Villa dake Abuja, yau Jumu'a.

Zamu tabbatar an jawo matasa a jiki - Buhari

Bugu da kari, Buhari ya jaddada cewa APC zata tabbatar an saka matasa a kowane mataki domi. su bada gudummuwar su.

Ya ce:

"Zan goyi bayan zakakurai kuma waɗan da suka shirya daga cikin matasa, waɗan ke neman wasu mukaman jam'iyya a babban gangami dake tafe."

Kara karanta wannan

2023: Abu ɗaya ya rage wa Shugaba Buhari wanda zai bar baya mai kyau, Tambuwal

"Yana daga cikin manufofin da muka sa a gaba mu tabbatar da gina jam'iyya mai kwari da dogon zangi ta hanyar mutanen da zamu miƙa wa ragamar tafiyar da ita."
"Ya kanata a kara karfafa wa mutane masu hazaka da juriyar aiki wajen tabbatar da gina hanya mai ɗorewa."

A wani labarin kuma Hukumar jin dadin yan sanda ta jinkirta ɗaukar mataki kan Abba Kyari saboda wasu dalilai

Hukumar jin dadin yan sanda PSC ta bayyana cewa a halin yanzun ta jinkirta ɗaukar mataki kan Abba Kyari sabida wasu dalilai.

Hukumar ta sanar da cewa zata jira har sai an kammala bincike, kuma ta baiwa yan sanda wa'adin mako biyu su kawo rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262