'Ka ga haske', Lawan ya jinjina wa Bwacha, Sanatan Taraba da ya fice daga PDP ya koma APC

'Ka ga haske', Lawan ya jinjina wa Bwacha, Sanatan Taraba da ya fice daga PDP ya koma APC

  • Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya yi wa Emmanuel Bwacha, sanata mai wakiltar Taraba da kudu barka bayan komawar sa jam’iyyar APC
  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari da kan sa ya karbi Bwacha zuwa jam’iyyar yayin wata kwarya-kwaryar liyafa da aka yi a fadar shugaban kasa da ke Abuja a makon da ya gabata
  • An karanto wata wasika a gaban majalisar dattawa a ranar Talatar da ta gabata wacce ta bayyana yadda sanatan ya sauya sheka da ga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC

FCT, Abuja - Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya yi wa Emmanuel Bwacha, sanata mai wakiltar Taraba ta kudu, barka da komawa jam’iyyar APC, The Cable ta ruwaito.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da kan sa ya karbi Bwacha zuwa jam’iyyar a wata liyafa karama da aka yi a fadar shugaban kasa a makon da ya gabata.

Kara karanta wannan

Ba kullum ake kwana a gado ba: PDP ba za ta ba Atiku takara a 2023 ba – Tsohon Gwamna

'Ka ga haske' - Lawan ya jinjina wa Bwacha, Sanatan Taraba da ya koma APC
Haske ya zo maka, furucin Lawan ga Bwacha, sanatan Jihar Taraba bayan ya koma APC. Hoto: The Cable
Asali: Twitter

An karanto wata takarda wacce sanatan ya bayyana wa kowa batun sauya shekar sa daga jam’iyyar PDP zuwa APC a cikin majalisar dattawa ranar Talata.

Ya ce ya bar PDP ne saboda rabuwar kawunan ‘yan jam’iyyar a jiharsa

A takardar kamar yadda The Cable ta bayyana, wacce Lawan ya karanta, Bwacha ya ce ya bar jam’iyyar PDP ne saboda rabuwar kawunan da ya yi yawa a reshen jam’iyyar na jiharsa.

Bayan kammala karatun wasikar, Lawan ya kwatanta batun yanke shawarar da Bwacha ya yi a matsayin abinda ya dace.

Kamar yadda ya ce masa:

“Ina taya ka murna akan yadda ka dauki hukunci mai kyau. Abinda ka yi a nan yana nuna cewa addu’ar mutanen yankin ka da ka samar wa da kayan more rayuwa ta amsu. Saboda sun yi maka fatan ganin haske kuma yanzu ka gan shi.”

Kara karanta wannan

Babbar magana ta fito: Shugaban PDP na jihar Kudu ya sauya sheka zuwa APC, ya fadi sirri

Yanzu haka APC tana da sanatoci 70 kenan yayin da PDP take da 38

Komawar Bwacha jam’iyyar APC na nuna cewa sanatoci 70 ne yanzu haka ke karkashin inuwar jam’iyyar, yayin da PDP ta ke da 38 sai YPP da take da daya rak.

Komawar sa na nufin ya rasa matsayin sa na Principal Officer na majalisar, kuma sauran sanatocin PDP ne yanzu haka za su yanke hukuncin wanda zai maye gurbin sa.

2023: Za mu bi didigin inda ƴan takara suke samo kuɗi, za mu sa ido kan asusun bankin ƴan siyasa, INEC

A wani rahoton kun ji cewa Hukumar zabe mai zaman kanta na Najeriya, INEC, ta aika da muhimmin sako ga yan siyasa da jam'iyyun siyasa gabanin babban zaben shekarar 2023.

Hukumar ta sha alwashin cewa za ta saka idanu a kan 'yan siyasa da jam'iyyun siyasa domin gano inda suke samo kudade domin yakin neman zabe, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Okorocha ya gana da Buhari kan kudirinsa na son zama magajinsa

Shugaban INEC na kasa, Farfesa Mahmood Yakubu, wanda ya bayyana hakan yayin wani taro da hukumar zaben ta shirya a Abuja, ranar Juma'a 21 ga watan Janairu, kuma ya ce hukumar za ta saka ido kan yadda aka hada-hadar kudade ranar zabe don dakile siyan kuri'u, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164