Sauya Sheka: Shugabannin majalisa biyu da wasu jiga-jigan PDP zasu koma APC
- Da yuwuwar sauya shekar Sanata Emmanuel Bwacha zuwa APC ya zama babban alheri a siyasar jam'iyyar reshen jihar Taraba
- Tsofaffin shugabannin majalisar dokokin Taraba biyu da kuma wasu yan majalisu uku na shirin sauya sheka zuwa APC
- A ranar Alhamis da ta gabata, Sanata Bwacha ya gana da shugaba Buhari a Aso Rock kan dalilin ficewarsa daga PDP
Taraba - Bayan sauya shekar Sanata Emmanuel Bwacha, daga PDP zuwa APC, tsaffin shugabannin majalisar jihar Taraba biyu, da mambobi uku zasu koma APC yau.
Jaridar Leadership ta rahoto cewa Bwacha ya kaiwa Buhari ziyara fadarsa ranar Alhamis, domin shaida masa dalilim ficewa daga PDP, da kuma shigowarsa APC.
Mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawan Najeriya ya zargi gwamnan Taraba, Darius Ishaku, da tilasta masa barin PDP.
Rahoto ya tattaro cewa shugabannin majalisar dokokin Taraba, Hon. Peter Abel Diah da Mark Bako Useni, suna cikin waɗanda za su sauya sheka zuwa APC a yau.
Sauran yan majalisun Taraba da ka iya bin sahun Bwacha sun haɗa da, mai wakiltar Karim II a majalisar jiha, Honorabul Charles Meijankai.
Sauran sun haɗa da, Hon. Gembo Meikudi, wanda ke wakiltar Bali I, da kuma Honorabul Josiah Aji, mai wakiltar mazaɓar Wukari II.
Yaushe zasu tabbatar da sauya sheƙar su?
Da muka tuntube shi kan sahihancin labarin, Honorabul Diah, yace:
"Ku sanya ido kuga yadda lamarin zai faru ranar Litinin. Meyasa kuke gaggawa ne, baki ɗaya lamarin zai faru a zaman majalisa."
"Ba zan faɗi masu sauya sheka ba ko wani mataki kan haka ba, kawai ku jira kuga abin da zai faru daga farko zuwa ƙarshen zaman majalisa na ranar Litinin."
Mark Bako Useni, wanda ke wakiltar mazaɓar Takum II, kuma tsohon kakakin majalisa yace:
"Mai yuwu wa wannan batun sauyan shekan a majalisar dokokin jihar ne yake hana wasu bacci a jihar Taraba."
"A karan kaina ba zan iya ce muku ga abin da zai faru ba a majalisar dokoki gobe Litinin ba. Yanzu da nake magana da ku na fita a duba lafiya ta, ku jira kuga abin da zai faru a zaman Litinin ɗin."
A wani labarin kuma Bayanai sun fito kan tattaunawa tsakanin mataimakin shugaban kasa, Farfesa Osinbajo, da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
Alamu masu karfi sun tabbatar da cewa jam'iyyar APC ta fara zawarcin tsagin Sanata Rabiu Kwankwaso na PDP.
Tsohon gwamnan Kano, Sanata Kwankwaso, na ɗaya daga cikin manyan yan siyasa masu dumbin magoya baya musamman a arewa.
Asali: Legit.ng