Siyasar Kano: An yi zaman sulhu tsakanin bangaren Ganduje da Shekarau, an cimma matsaya

Siyasar Kano: An yi zaman sulhu tsakanin bangaren Ganduje da Shekarau, an cimma matsaya

  • Kwamitin riko na APC ta kasa ta cimma matsaya a kan rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar reshen jihar Kano
  • A yau Lahadi, 6 ga watan Fabrairu ne aka sake zama tsakanin bangaren Gwamna Abdullahi Ganduje da Sanata Ibrahim Shekarau bayan tattara bayanai da kwamitin ya yi
  • Daga cikin matsayar da aka cimma shine cewa dole ne kowani bangare ya yi aiki tare da dan uwansa domin samun nasara

Kano - Kwamitin riko na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa karkashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya cimma matsaya a kan rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam’iyyar reshen Kano.

Sashin Hausa na BBC ya ruwaito cewa a ranar Asabar, 5 ga watan Fabrairu, kwamitin ya kira taron gaggawa tsakanin bangarorin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Ibrahim Shekarau.

Kara karanta wannan

Dukiyar sata: Yadda Ministan Buhari ya lallaba, ya ba kamfani kwangilar makudan Biliyoyi

Hakan ya biyo bayan tattara bayanai da kwamitin ya yi a ranar Talata, 25 ga watan Janairu.

Siyasar Kano: An yi zaman sulhu tsakanin bangaren Ganduje da Shekarau, an cimma matsaya
Siyasar Kano: An yi zaman sulhu tsakanin bangaren Ganduje da Shekarau, an cimma matsaya Hoto: BBC Hausa
Asali: UGC

Rahoton ya kuma kawo cewa kakakin Shekarau, Dr Sule Ya’u ya bayyana cewa an cimma matsaya, sai dai ya ce akwai karin bayanai da za a samu daga kwamitin a ranar Litinin.

Sule ya ce:

“A batutuwan da aka gabatarwa bangarorin guda biyu akwai cewa jam’iyya ba ta sashi day aba ce, sannan kuma cewa ya zama dole kowani bangare ya tafi da dan uwansa don cimma nasara.”
“Amma za a gabatar da cikakkun shawarwarin a ranar Litinin, kuma ana sa ran duka bangarorin biyu za su mika wuya ga wannan yarjejeniya wadda za ta samar da mafita a jihar.”

A nashi bangaren, tsohon shugaban Majalisar jihar Kano, Hon Kabiru Alhasan Rurum, wanda ke biyayya ga Gwamna Ganduje ya ce ga dukkan alamu komai ya zo karshe.

Kara karanta wannan

Hotuna: Jam'iyyar APC ta yi babban kamu, fitaccen sanata ya bar PDP ya shigo APC

Rurum ya ce:

“Muna da kyakkyawan zaton wannan lamar yazo karshe domin, uwa daya muke uba daya muke.
"Abin da muke zaton ji maslaha daga kwamitin riko na wannan jam’iyya, saboda duka bangarorin mun yi wa juna wahala a baya.”

Siyasar Kano: Tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano, Rimin-Gado, ya koma PDP

A wani labarin, dakataccen shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, Muhyi Rimin-Gado, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar People Democratic Party (PDP) gabannin zaben 2023.

Rimin-Gado ya bayyana cewa ya mika takardar neman shiga PDP ta yanar gizo yayin da yake sa ran yin rijista a unguwarsa ta karamar hukumar Rimingado a watan Fabrairu, jaridar Punch ta rahoto.

Tun bayan dakatar da shi da gwamnatin jihar Kano ta yi a ranar 5 ga watan Yulin 2021, fastocin tsohon shugaban na hukumar yaki da cin hanci sun karade unguwanni a Kano inda suke ayyana aniyarsa na takarar gwamna a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Rikicin Kano: Mala Buni ya yi zama da Shekarau da manyan APC da ke fada da Ganduje

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng