Dalilai 4 da suka san a raba jiha da Buhari, Saraki ya fasa kwai
Daga karshe tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya magantu a kan dalilin da yasa ya raba jiha da shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.
Ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, 5 ga watan Fabrairu, a yayin wata tattaunawa ta Twitter wanda daya daga cikin jagororin zanga-zangat #EndSARS, Rinu Oduala ya shirya.
Saraki, shugaban majalisar dattawa a majalisa ta takwas daga 2015 zuwa 2019 ya amsa tambayoyi daga mutane kan zaben 2023 da kuma harkokin siyasa na baya.
A cewarsa, ya goyi bayan takarar shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2015 saboda yana burin ganin chanji a kasar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Tsohon gwamnan na jihar Kwara ya ambaci abubuwan kamar haka:
1. Tsangwama
Saraki ya yi ikirarin cewa ya sha tsangwama a lokacin da yake matsayin shugaban majalisar dattawa saboda ya tsaya tsayin daka don ganin yancin majalisar dokokin tarayyar.
Mai niyar tsayawa takarar shugabancin kasar ya bayyana cewa dukkanin wahalar da ya sha ya kasance saboda majalisar dokokin tarayya a karkashin jagorancinsa bata yarda da yiwa bangaren zartarwa alfarma ba.
2. Gwamnatin shugaban kasa Buhari
Saraki ya bayyana cewa gazawar gwamnatin Buhari karkashin APC wajen kawo chanjin da ake bukata ne ya sa shi barin jam'iyyar.
3. Alkawarin chanji
A cewarsa, ya zata ajandar chanji na jam'iyyar za ta taimake shi wajen cimma manufofinsa don amfanin yan Najeriya gaba daya.
4. Ba a cimma manufar chanji ba
Tsohon shugaban majalisar dattawan ya ce ya bar tafiyan ne a lokacin da ya lura cewa manufar chanji da jam'iyyar ta yiwa yan Najeriya alkawari ba a gani a kasa ba.
IBB ya bayyana goyon bayansa kan takarar shugabancin kasa da Saraki zai fito
A gefe guda, mun kawo cewa tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya taki sa' a saboda tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida ya bayyana goyon bayansa ga burinsa na maye gurbin shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2023.
Janar Babangida ya yi martani ne kan bukatar da wakilan Abubakar Bukola Saraki da suka samu jagorancin shugaban kungiyar kamfen din sa, Farfesa Hagher Iorwuese da darakta janar, Osaro Onaiwu wadanda suka je har gidan IBB da ke Minna domin neman goyon baya.
Babangida wanda ya kasa boye kaunarsa ga Saraki, ya kasa rufe baki don kai tsaye ya ce Saraki tamkar bindigar yaki ce mai harba kanta, a takaice hakan ne kwatancen Saraki, Vanguard ta ruwaito.
Asali: Legit.ng