Da dumi-dumi: Mataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa ya sauya sheka zuwa APC

Da dumi-dumi: Mataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa ya sauya sheka zuwa APC

  • Mataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa, Emmanuel Bwacha, ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC
  • Bayan sauya shekar nasa, Bwacha ya hadu da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa a ranar Alhamis, 3 ga watan Fabrairu
  • Shugaban kwamitin riko na APC kuma gwamnan Yobe, Mai Mala Buni ne ya gabatar da Bwacha a gaban shugaban kasar

Sanata mai wakiltan Taraba ta kudu kuma mataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa, Emmanuel Bwacha, ya sauya sheka daga jam'iyyar Peoples Democratic Party zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tarbi Bwacha zuwa APC a hukumance a fadar shugaban kasa a ranar Alhamis, 3 ga watan Fabrairu, inda ya mika masa tutar jam'iyyar mai mulki.

Kara karanta wannan

Zargin siyasa: Majalisa ta tabbatar da nadin kwamishinan INEC da ake zargin yar APC ce

Da dumi-dumi: Mataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa ya sauya sheka zuwa APC
Da dumi-dumi: Mataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa ya sauya sheka zuwa APC Hoto: @Buharisallau1
Asali: Twitter

Shugaban kwamitin rikon kwarya na APC kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ne ya gabatarwa Buhari da Bwacha a fadar Villa da ke Abuja.

Mai ba shugaban kasa shawara a kan kafofin sadarwa ta zamani, Buhari Sallau ne ya sanar da batun sauya shekar sanatan a shafinsa na Twitter.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya rubuta a shafin nasa:

"Shugaban rikon kwarya na APC kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, Shugaban kasa Muhammadu Buhari da sabon mambar jam'iyyar, mataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa, Sanata Emmanuel Bwacha, a yayin gabatar da sanatan wanda ya sauya sheka zuwa jam'iyyar daga PDP a baya-bayan nan a fadar shugaban kasa."

Hotuna: Jam'iyyar APC ta yi babban kamu, fitaccen sanata ya bar PDP ya shigo APC

A wani labari makamancin haka, mun ji cewa wani fitaccen sanata mai wakiltar Yobe, Sanata Mohammed Hassan, a ranar Talata, 1 ga watan Fabrairu, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar adawa ta PDP.

Kara karanta wannan

Takara a 2023: Sule Lamido ya ce Tambuwal ne ya fi dacewa ya gaji Buhari, ya fadi dalili

Sanata Hassan ta shafin sada zumunta na Facebook ya ce ya dauki matakin ne da yammacin ranar Talata sannan ya ziyarci shugaban kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar APC na kasa (CECPC), Gwamna Mai Mala Buni kan shawarar tasa.

Daya daga cikin magoya bayan Sanata Hassan, Abdullahi Yakubu, a shafukan sada zumunta wanda ya mayar da martani game da ci gaban ya ce jam’iyya mai mulki ta samu dawowar jigonta cikinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng