Takara a 2023: Kungiyar CAN ta yi watsi da Yahaya Bello, ta yi karin bayani a kansa
- Kungiyar CAN a jihohin arewa 19 da Abuja ta yi watsi da rade-radin cewa ta tsayar da Yahaya Bello a matsayin dan takarar shugaban kasa da zata marawa baya a zaben 2023
- CAN ta ce a tarihin zaben kasar bata taba goyon bayan wani mai neman mukamin shugabanci ba kuma ba za ta fara ba a yanzu
- Ta ce aikinta ga Najeriya shine yiwa kasar addu'a a matsayinta na kungiyar addini
Abuja - Kungiyar Kiristocin Najeriya a jihohin arewa 19 da Abuja ta yi watsi da rahotannin cewa ta marawa takarar shugaban kasa na Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi baya a zaben 2023.
CAN ta bayyana hakan ne a wata sanarwar da ta fitar bayan wani gagarumin taro da ta gudanar a otal din Excel da ke Abuja, PM News ta rahoto.
Buhari ba zai iya tafiyar mota babu shiri ba, Fadar shugaban kasa ta yi wa PDP martani kan ziyarar Zamfara
Jami'in hulda da jama'a na kungiyar CAN a jihohin arewa da Abuja, Chaplain Jechonia Gilbert, ya ce kungiyar bata taba tsayar da wani mutum don darewa wata kujerar shugabanci a tarihin zabe a Najeriya kuma ba za ta aikata hakan ba a zaben 2023.
Punch ta nakalto kungiyar na cewa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Muna so mu yi karin haske kan rahotannin baya-bayan nan a wasu jaridun yanar gizo cewa kungiyar CAN reshen arewa ta tsayar da Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi a matsayin dan takararta na zaben 2023.
"A tarihi, kungiyar CAN ta arewa bata taba tsayar da wani mutum don neman matsayin shugabanci a tarin zaben Najeriya kuma ba za ta aikata hakan ba a wannan lokaci. Aikinmu a Najeriya a matsayinmu na kungiyar addini shine yiwa kasar addu'an zaman lafiya da karfafawa mambobin gwiwar shiga a dama da su a tsarin damokradiyya don ci gaban kasa.
"A matsayin kungiya mai dumbin mabiya da kuma mambobinta da ke jam'iyyun siyasa mabanbanta, rashin tunani ne ayi hasashen cewa mun tsayar da wani mutum wanda bai ma mallaki tikitin takara na kowace jam'iyya ba a matsayin dan takararmu na zaben shugaban kasa a 2023.
"Muna kira ga jama'a da su yi watsi da irin wannan rahoto domin bai taba zama tunanin kungiyar CAN na arewa ba. Ba a taba yin irin wannan ganawarba da shugabannin CAN na arewa don zartar da wannan hukunci.
“Bayan INEC ta fitar da jadawalin zabe, mun hadu a nan ne domin bayar da gudunmawarmu wajen gina kasa ta hanyar umurtar shugabanninmu na shiyyoyi uku na Arewa da su koma su tara mambobinsu da su fito gaba daya domin yin rajista don su samu damar shiga zaben 2023 mai zuwa.
"An yi taron ne domin hada rahotanni daga shiyoyi game da lamarin tsaro a jihohi daban-daban da suka hada yankin da nufin taimakawa shugabancin CAN na arewa wajen yin jawabi ga kasar game da matsalolin rashin tsaro a arewa."
2023: Malaman addinin Musulunci da Kirista fiye 1,000 sun yi taron yi wa gwamnan APC addu’o’in samun nasara
A wani labarin, mun ji cewa fiye da malaman addinai na Kirista da musulunci sun taru a Abuja ranar Juma’a suna nuna goyon baya ga gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello don ya zama shugaban kasa a 2023, The Nation ta ruwaito.
Malaman sun ce Bello ne ya dace da ya gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari a shekarar 2023 sakamakon ayyukan da suka gani ya yi a Jihar Kogi.
A cewar su, Bello tsayayyen mutum ne wanda zai iya tabbatar da adalci ga ‘yan Najeriya idan ya zama shugaban kasa.
Asali: Legit.ng