Buhari ba zai iya tafiyar mota babu shiri ba, Fadar shugaban kasa ta yi wa PDP martani kan ziyarar Zamfara
Fadar shugaban kasa tace tsokacin da jam'iyyar PDP tayi game da fasa kai ziyara Zamfara da shugaba Muhammadu Buhari yayi alamar neman rigima ne da tsegumi.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shirya kai wa Zamfara ziyara a ranar 27 na watan Janairu don tattaunawa game da matsalar rashin tsaro a jihar sannan ya jajanta wa mutane a kan hare-haren da aka kai kwanan nan a karamar hukumar Anka da Bukkuyum.
Sai dai, yayin da aka fara shirye-shiryen tarbar sa, Bello Matawalle, gwamnan Zamfara, ya bayyana cewa shugaban kasar zai canza lokacin ziyarar don matsalar rashin ganin da jirgi ke fama da shi saboda buji.
Yayin zantawa a gidan talabijin da mazauna Zamfara a ranar, Buhari ya bayyana takaicin sa na fasa zuwa jihar, inda ya ce abun "bai masa dadi ba".
Yayin tsokaci, PDP ta ce Buhari ya soke tafiyar ne saboda tsoron kai masa farmaki, ya kamata ya je ko a mota ne.
Yayin maida martani a wata takarda da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya fitar a ranar Lahadi, ya ce sukar Buhari da PDP ke yi ya na nuna jam'iyyar ba ta fahimci meye mulkin kasa ba duk da ta kwashe shekaru 16 ta na mulki.
"Kamar yadda shugaban kasar yayi bayani na musamman ga mutanen jihar, canjin yanayin gari ne babba kuma dalilin sa guda da yasa ya soke ziyarar," kamar yadda takardar ta kunsa.
"Ba bakon abu ba ne don jirgi ya fasa tashi saboda matsalar yanayin gari, ta yuwu saboda iska ko hadari, buji ko guguwa kamar yadda mu ka ji a ranar Alhamis yadda yawancin biranen arewa har da Gusau, babban birnin jihar Zamfara.
"Da yawan biranen nan an san yadda suke fama da matsalar rashin gani lokacin hunturu kamar yadda muke ciki," yace
Takardar ta kara da cewa:
"Nisan kilomita 1 shi ne tsayayyan mafi karancin ganin, amma na Gusau a ranar ya sha bambam, wannan mafi karancin rashin ganin na mita 1000 ya yi kasa, ya na ta canzawa tsakanin mita 300-400.
"Sukar shugaban kasa, musamman wanda jam'iyyar adawa ta PDP ke yi na kin tafiya da yayi zuwa Gusau a mota, nisan kimanin kilomita 200 yana nuna ko dai rashin fahimtar shugabancin kasa musamman ga jam'iyyar da ta kwashe shekaru 16 tana mulki, ko kuma tsabaragen neman rikici. Ko ma meye, dole komai ya na da iyaka."
"A duniya baki daya, shugaban kasa, mai ci ko kuma wanda ya sauka daga mukamin ba zai kawai fada mota ya je duk inda yake so ba, a kowanne lokaci a rana. Misali kasar Amuruka, akwai dokar da ta dade tun 1958 wadda ta hana tsofaffin shugabanni tafiya kan titi ba tare da tabbatar da tsaro ba.
"Maganar da PDP ta yi na sukar shugaban kasa a kan fasa zuwa Gusau ba tare da dubi da hakan ba, abun kunya ne ga jam'iyyar da ta yi shugabancin kasa. Ina nasarorin su?
"Abun takaici ne ga kasa a ce tsabar damuwa ta tilasta PDP, ita a dole jam'iyyar adawa, ta ratayar da rayuwarta ta hanyar zabga karairayi. Inda tarin karyace-karyacen su yake kara habaka a kullum.
"A duk lokacin da aka samu gyaruwan yanayin gari da sauran abubuwa, zai dawo sannan a lokacin da ya dace ya karasa abubuwan da yayi niyya, " Garba Shehu yace.
Asali: Legit.ng