Bikin sauya sheka: Dan majalisan APC ya tsallake, ya koma tsagin adawa ta PDP
- Jam'iyyar APC ta rasa daya daga cikin mambobinta na majalisar wakilai bayan ya sauya sheka
- Dan majalisar, Yahaya Fatuba daga jihar Gombe ya koma jam'iyyar adawa ta PDP
- Ya ce rashin gudanar da zaben fidda gwani na gaskiya a jihar Gombe shine ya sa shi tsallake jam'iyyar mai mulki
Abuja - Wani mamba a majalisar wakilai, Yahaya Fatuba daga jihar Gombe ya bar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
Wata wasika da kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya karanto a zauren majalisar ta nakalto dan majalisar yana cewa rikice-rikicen cikin gida da ya dabaibaiye jam'iyyar ne ya sa shi barinta.
A cikin wasikar, Fatuba ya bayyana cewa APC ba ta gudanar da sahihin zaben fidda gwani ba a jihar Gombe, Vanguard ta rahoto.
Dan majalisa daga Gombe ya lissafo gwanayensa, ya ce daya daga cikinsu ne ya cancanci ya gaji Buhari
Da yake martani, shugaban marasa rinjaye a majalisar, Ndudi Elumelu ya jinjinawa ci gaban, yayin da ya yabama kakakin majalisar kan samun karfin gwiwar karanto wasikar sauya shekar.
Elumelu ya hakan alamu ne da ke nuna cewa wasu karin yan majalisa da dama za su dawo cikinsu "inda suka fi wayo" saboda jam'iyyar APC na da tsagi da yawa da shugabannin tsagi-tsagi a fadin kasar.
Ya bayyana kakakin a matsayin namijin duniya da ya karanto wasikar sauya shekar, rahoton Independent.
Kakakin majalisar ya ce abu ne da ya zama masa dole karanto wani wasika da ya shigo zauren koda kuwa daga ina ya fito.
Ado Doguwa ya samu karuwar 'diya na 28, ya lashi takobin haifan 30 kafin 2023
A wani labari na daban, Allah ya azurta Shugaban masu rinjayen majalisar wakilan tarayya, Alhassan Ado Doguwa, da karuwar 'da na ashirin da takwas (28) daga daya daga cikin matansa hudu.
Ado Doguwa ya bayyana hakan ranar Talata a zauren majalisa yayinda takwaransa, Hanrabul Ndudi Elumelu, ya taya sa murna, rahoton Tribune.
Dan majalisan ya yi alkawarin cewa ba zai daina hayayyafa ba saboda har yanzu da sauran karfinsa kuma zai haifi 30 kafin zaben 2023.
Asali: Legit.ng