2023: Ƙungiyar kare hakkin musulmi ta caccaki Afenifere kan goyon bayan Tinubu

2023: Ƙungiyar kare hakkin musulmi ta caccaki Afenifere kan goyon bayan Tinubu

  • Kungiyar kare hakkin musulmi, MURIC ta caccaki wata kungiyar yarabawa, Afenifere akan yadda ta ki amincewa ta goyi bayan takarar Bola Tinubu
  • Dama jigon jam’iyyar APC, Tinubu ya bayyana burinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023 da ke karatowa wanda Afenifere ta nuna rashin yardar ta
  • Darektan MURIC, Ishaq Akintola ya saki wata takarda ta ranar Talata inda ya ce kin goyon bayan Tinubu babban kuskure ne ga Afenifere

Kungiyar kare hakkin musulmi, MURIC, ta magantu dangane da maganganun kungiyar yarabawa ta Afenifere akan zarginta na kin goyon bayan jagoran jam’iyyar APC, Bola Tinubu dangane da burinsa na tsayawa takara a shekarar 2023, The Punch ta ruwaito.

A wata takarda wacce Shugaban MURIC, Ishaq Akintola ya saki ranar Talata mai taken, ‘Tinubu: MURIC Tasks Afenifere’ ya yi maganganu akan matsayar kungiyar yarabawan.

Kara karanta wannan

Shugaba a 2023: Fulani sun yi watsi da 'yan takara daga Arewa, sun fadi zabinsu

2023: Ƙungiyar kare hakkin musulmi ta caccaki Afenifere kan goyon bayan Tinubu
2023: Ƙungiyar MUROC ta caccaki Afenifere kan goyon bayan Tinubu. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

Punch ta ruwaito yadda shugaban Afenifere, Ayo Adebanjo ya ce kungiyar sa ba za ta bi bayan wani dan takarar shugaban kasa a 2023 ba har sai an sauya kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya koma tsarin karba-karba na yankuna.

Afenifere ta nuna rashin amincewarta da Tinubu

Yayin da aka tambayi Afenifere idan kungiyar za ta goyi bayan Tinubu, Adebanjo cewa ya yi, “Ban tabbatar ba kuma ba zan ce komai ba a halin yanzu. Ba na goyon bayan wani dan takara har sai an sauya kundin tsarin mulki.”

Sai dai MURIC ta ce ta yi mamakin yadda Afenifere har yanzu bata bayyana ra’ayin ta ba bayan makwanni biyu da Tinubu ya bayyana kudirinsa na tsayawa takara a 2023.

Kungiyar musulman ta saki takardar inda ta ce:

Kara karanta wannan

Magance tsaro: Tinubu ya bada tallafin miliyoyin Nairori ga jihar Neja

“Babban kuskure Afenifere ta ke yi na janye jiki daga Tinubu saboda ta goyi bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari. Afenifere gurguntacciyar siyasa take yi kuma babu tunani balle kishi a cikinta.
“Abubuwan da Tinubu ya yi ga kasa kadai sun isa a amince da shi kuma sai mutum ya nuna kansa kafin duk wani dan kasa ya rungume shi. Ya kamata Afenifere ta yi wayau.”

Ya kamata Afenifere ta gane cewa da arziki a garin wani gara a naku

Ya kara da cewa:

“Ya kamata Afenifere ta koyi wani abu daga wurin Ibo na nuna kishin ‘yan uwansu. A kalla Bayerabe ya nuna ra’ayinsa akan tsayawa takara don haka ya kamata ta bi bayansa.
“Ya kamata Afenifere ta sauya salon siyasarta. Kuma ya kamata a dinga saka alheri da alheri. Bai dace kungiyar yarabawa ta saki nata ko kuma ta ki bin bayan kowa yayin da kowa yake mara wa nasa baya.”

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Tinubu ya dura Neja, ya shiga ganawa da IBB kan batun takara a 2023

2023: Za mu bi didigin inda ƴan takara suke samo kuɗi, za mu sa ido kan asusun bankin ƴan siyasa, INEC

A wani rahoton kun ji cewa Hukumar zabe mai zaman kanta na Najeriya, INEC, ta aika da muhimmin sako ga yan siyasa da jam'iyyun siyasa gabanin babban zaben shekarar 2023.

Hukumar ta sha alwashin cewa za ta saka idanu a kan 'yan siyasa da jam'iyyun siyasa domin gano inda suke samo kudade domin yakin neman zabe, Vanguard ta ruwaito.

Shugaban INEC na kasa, Farfesa Mahmood Yakubu, wanda ya bayyana hakan yayin wani taro da hukumar zaben ta shirya a Abuja, ranar Juma'a 21 ga watan Janairu, kuma ya ce hukumar za ta saka ido kan yadda aka hada-hadar kudade ranar zabe don dakile siyan kuri'u, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164