Tanko Yakasai: 'Yan Arewa ba sa tsinana komai a Najeriya, a ba 'yan kudu mulki a 2023

Tanko Yakasai: 'Yan Arewa ba sa tsinana komai a Najeriya, a ba 'yan kudu mulki a 2023

  • Tanko Yakasai ya bayyana cewa, rashin adalci ne dan Arewa ya maye gurbin shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023
  • Dattijo Tanko Yakasai ya ce dole mulki ya koma Kudu domin shugabannin Arewa tun da suke mulkin kasar ba su taba tsinana komai ba
  • Yakasai ya ce a cikin dukkan masu neman tsayawa takarar shugabancin kasa a jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu shi ne ya fi cancanta

Jihar Kano - Tanko Yakasai, wani dattijon kasa daga jihar Kano a ranar Lahadi, 23 ga watan Janairu ya bayyana goyon bayansa ga dan Kudu ya maye gurbin shugaban kasa Muhammadu Buhari a karshen wa’adinsa a 2023.

Daily Trust ta ruwaito cewa, dattijon dan shekaru 96 da haihuwa, ya ce ba zai zama adalci ba a ce yankin Arewa ya ci gaba da yin mulki duk da yunkurin da 'yan Kudu ke yi na neman kujerar.

Kara karanta wannan

Ban yi wa Buhari kamfen ba, hotunansa kawai na wallafa, Dele Momodu

Alhaji Tanko Yakasai ya magantu kan mulkin 'yan Kudu
Rashin adalci ne dan arewa ya sake mulkar Najeriya a 2023, Tano Yakasai ya fadi dalili | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Yakasai, daya daga cikin manyan masu sukar gwamnatin Buhari yana da ra'ayin cewa zai zama an zalinci 'yan Kudu idan dan Arewa ya hau mulki a 2023.

Dattijon ya ce a tsawon shekarun da ’yan Arewa suka yi mulki a kasar nan ba su tabuka komai ba, kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tinubu ne gwani na

Ya ci gaba da cewa, a cikin dukkan wadanda suka bayyana aniyarsu ta tsayawa takara daga yankin kudu, jagoran jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya fi cancanta.

Yakasai ya ce:

“Ta yaya za a yi a kullum mu ’yan Arewa ne za mu ke mulki? Babu adalci a cikin wannan lamari, mu yi mulki, su (Kudu) su yi mulki shi ne adalci.
“Duk da cewa a tsawon shekarun da ’yan Arewa suka yi mulki ba mu ga komai ba, me za mu ce wa jama’a? Me za mu nuna wa ‘yan Najeriya da suka amfana ko za su amfana domin su ba mu kuri’unsu?.”

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Nnamdi Kanu ya ce shi ba dan IPOB ba ne, bai ma da alaka da ita

Gwamnan Kudu ya zugo Gwamnoni domin a yaki Atiku, Saraki da manyan Arewa a PDP a 2023

A wani labarin, rahotanni daga Daily Trust sun nuna cewa Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya fito gadan-gadan domin ya yaki kusoshin PDP daga Arewacin Najeriya.

Nyesom Wike yana neman yadda zai jikawa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, Bukola Saraki, da irinsu Rabiu Kwankwaso aiki a zaben 2023.

Majiya ta shaidawa jaridar cewa gwamnan na jihar Ribas wanda kusan shi kadai ne yake daukar dawainiyar jam’iyyar hammayar, ya fara tuntubar abokan aikinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.