Mambobin APC sama da 11,000 sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar PDP, APC ta fusata
- Yayin da babban zaɓen 2023 ke kara ƙaratowa, dubbannin mambobin APC sun fice daga cikin jam'iyyar, sum koma PDP
- Lamarin baiwa APC daɗi ba, inda kakakin APC reshen jihar Gombe, ya maida zazzafan maratani ga waɗan da suka sauya shekan
- Yace mutanen sun ɗauki wannan matakin ne saboda ba su da ƙarfin samun tikitin takara a babban zaben 2023
Gombe - Jaridar Punch ta rahoto cewa aƙalla mambobin jam'iyyar APC mai mulki 11,000 a ƙaramar hukumar Funkaye, jihar Gombe, sun sauya sheka zuwa PDP.
Sai dai lamarin baiwa APC daɗi ba, inda ta maida martaani da cewa sun sauya sheƙa ne saboda ba za su iya samun tikitin takara ba a zaɓen 2023 dake tafe.
Da yake martani kan lamarin, kakakin jam'iyyar APC reshen jihar Gombe, Moses Kyari, yace mutanen sun sauya sheƙa ne saboda wasu dalilai na ƙashin kansu.
Mista Kyari yace:
"Sun yi tunanin ba zasu iya samun tikitin takara ba a zaɓen 2023, shiyasa suka zaɓi komawa PDP."
Meyasa suka sauya sheka zuwa PDP?
Da yake jawabi a wurin karɓan masu sauya shekan ranar Asabar, jigon PDP, Abubakar Abubakar, ya tabbatar wa mutanen ba zasu shiga matsala ba kamar yadda suka fuskanta a APC.
Abubakar, wanda tsohon ɗan majalisar wakilai ne, ya bayyana cewa mutanen sun ɗauki matakin koma wa PDP ne saboda tsohuwar jam'iyyarsu ta yi watsi da su.
Abubakar ya ce:
"A baya ni mamba ne a APC amma na guje ta saboda rashin haɗin kai da kuma gazawar gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na jihar Gombe."
Abubakar ya ƙara da cewa gwamnan ya yi watsi da baki ɗaya yan siyasar da suka hana idon su bacci har ya samu nasarar kaiwa wannan matakin.
A wani labarin na daban kuma Aisha Buhari ta bayyana babban hukuncin da take goyon bayan a yanke wa wanda ya kashe Hanifa a Kano
Matar shugaban ƙasa, Aisha Muhammadu Buhari. ta nuna goyon bayanta kan irin hukuncin da ya dace a yanke wa makashin Hanifa
Uwar gidan shugaban tace tana goyon bayan hukuncin da Shiekh Abdallah Gadon Ƙaya, ya yi kira a yanke wa mutumin da ya kashe yarinyar.
Asali: Legit.ng