2023: Daga ƙarshe, Yahaya Bello ya sanar cewa ya shiga jerin masu son gadon kujerar Buhari
- Daga karshe, gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, ya bayyana niyarsa na fitowa takarar shugaban kasa a 2023
- Gwamnan ya ce idan an zabe shi a matsayin shugaban Najeriya, zai dora a kan abubuwan alheri da gwamnatinsa ta yi a Kogi
- Wasu daga cikin yan majalisa na jam'iyyar APC a arewa maso gabas sun goyi bayan takarar gwamnan na Kogi
Jihar Bauchi - Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, ya bayyana niyyarsa na fitowa takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar All Progressives Cogress, (APC).
Bello ya yi wannan kadamarwar ne a Bauchi a ranar Alhamis 20 ga watan Janairu yayin da ya ke gana wa da wasu yan majalisar APC da kungiyoyin mata a yankin yayin taro na siyasa a jihar.
Jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito cewa gwamnan na Kogi wanda ya yi wa masu taron jawabi ta fasahar murya da bidiyo na intanet ya ce:
"Ina gabatar da kai na domin takarar shugabancin kasa a 2023 karkashin jam'iyyar mu ta APC domin kasar nan tana bukatar shugabanci na gari daga matasa.
"Kamar yadda ku ke gani, muna tafiya sannu a hankali, ina bukatar goyon bayan ku, ina bukatar addu'ar ku domin mu yi nasara. Za mu dora kan ayyukan alherin da gwamnati mai ci yanzu ta yi."
Yan majalisu na jihohin Arewa sun mara wa Yahaya Bello baya
‘Yan majalisan dokoki daga yankin Arewa maso gabashin Najeriya da ke karkashin jam’iyyar APC sun yi wa Gwamna Yahaya Bello mubaya’a.
Jaridar Leadership ta fitar da rahoto a yau Juma’a, 21 ga watan Junairu 2022 cewa ‘yan majalisar bangaren sun bi sahun takwarorinsu na Arewa maso tsakiya.
A wata sanarwa da ta fito daga bakin ‘yan majalisan jihohin, sun bayyana goyon bayansu ga neman takarar shugabancin kasan da Gwamnan Kogi yake yi.
2023: Zan iya shugabancin Najeriya amma dai ban matsu ba, Orji Kalu
A wani labarin, bulaliyar Majalisar Dattawa, Orji Uzor Kalu, ya ce duk da a shirye ya ke da ya yi kamfen kuma zai iya shugabantar kasar nan, amma bai matse ya ce ai zama shugaban Najeriya ba, Daily Trust ta ruwaito.
Kalu, tsohon gwamnan Jihar Abia, ya yi wannan bayanin ne a ranar Laraba yayin amsa tambayoyi daga manema labarai a Majalisar Tarayya, washegarin da ya kai wa Buhari ziyara a fadarsa da ke Abuja.
A cewarsa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, takarar shugaban kasa hukunci ne ‘yan Najeriya zasu yanke sannan ko wacce jam’iyya zata zabi bangaren da za ta bai wa damar tsayawa takara, musamman jam’iyyar APC.
Asali: Legit.ng