Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ya fice daga jam'iyyar APC mai mulki

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ya fice daga jam'iyyar APC mai mulki

  • Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa kuma jigo a jam'iyyar APC mai mulki ya fice daga jam'iyyar, yace zai nemi tikiti a tsagin adawa
  • Mista Famuyibo, yace alamu sun nuna wanda gwamna ke so APC zata baiwa tikitin takarar gwamnan Ekiti a zaben dake tafe 2022
  • A cewarsa, babu dalilin da zai sa ya cigaba da zama a APC duba da bukata da burin al'umma a akan sa

Ekiti - Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin SDP, kuma jigon APC, Chief Reuben Famuyibo, ya fice daga jam'iyyar APC mai mulki, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Yace zai nemi tikitin takara a zaɓen gwamnan jihar Ekiti na ranar 18 ga watan Yuni, 2022 ƙarƙashin inuwar jam'iyyar Accord Party (AC).

Chief Reuben Famuyibo
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ya fice daga jam'iyyar APC mai mulki Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Mista Famuyibo, ya bayyana matakin da ya ɗauka ne yayin zantawa da manema labarai a Ado-Ekiti, babban birnin jihar Ekiti, ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC a Arewa ya faɗi lokacin da zai bayyana kudirin takarar shugaban ƙasa a 2023

Tsohon ɗan takarar gwamna ƙarƙashin APC, ya soki tsohuwar jam'iyyarsa bisa ƙin baiwa ƴan takarar filin fafatawa har a fitar da ɗan takara ɗaya tilo.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Meyasa ya fice daga APC mai mulki?

Famuyibo yace ya ɗauki matakin ficewa daga APC ne saboda ya cimma burinsa a jam'iyyar AC, da kuma buƙatar mutane da masu ruwa da tsaki na ciki da wajen Ekiti kan ya tsaya takara.

Yace mutanen da suka amince masa da kuma ɗumbin magoya baya sun bukaci ya nemi tikitin takara a wata jam'iyya.

Fitaccen ɗan siyasan, haifaffen Ado-Ekiti, yace ya gano shirye-shiryen zaɓen fidda gwani a APC na tafiya ne kan tsarin wanda gwamna ke son ya gaje shi.

Dan haka ba bukatar cigaba da tafiya a haka, ya kuma bayyana cewa, "Ba zai yuwu mu cigaba da tafiya a haka ba, duba da manufofin mu ga jihar mu."

Kara karanta wannan

Babban ɗan kasuwa a Arewa ya sanar da shugaba Buhari kudirinsa na takarar shugaban ƙasa a 2023

A wani labarin na daban kuma Bola Tinubu ya bayyana babban abinda zai fara yi wa Talakawan Najeriya bayan zama shugaban ƙasa a 2023

Jagoran jam'iyyar APC na ƙasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya fara bayyana wa yan Najeriya manufofinsa bayan ɗarewa karagar mulki a 2023.

A cewarsa, da zaran ya ɗare karagar mulki a 2023, yan Najeriya sun gama kuka kan biyan kuɗin WAEC, zai biya wa kowane ɗalibi a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262