Shugabancin 2023: Manyan kalamai 4 da gwamnan PDP yayi game da takarar Tinubu
A yayin ziyarar da Bola Ahmed Tinubu ya kai jihar Oyo a ranar Asabar, 15 ga watan Janairu don yiwa gwamnati da mutanen jihar ta'aziyyar mutuwar babban basarake da Alao Akala, Gwamna Seyi Makinde ya yi wasu muhimman kalamai da zai zo kamar tuni ga Jagaban.
Gwamnan na Oyo wanda ya bayyana cewa Tinubu na kan turbar siyasa ba da gaba ba ya nuna godiya gare shi kan ziyartar jihar a lokacin da take juyayi.
Da yake magana musamman game da takarar tsohon gwamnan na Legas, Makinde ya bayyana abubuwa kamar haka:
1. Ka yi tunani kan dalilin ka na zuwa gidan gwamnatin Oyo
Makinde ya bayyana cewa akwai bukatar Tinubu ya tambayi kansa dalilinsa na zuwa gidan gwamnatin Oyo a daidai lokacin da jam'iyyun siyasa da yan takara ke gagarumin shirye-shirye gabannin zaben 2023.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Gwamnan na Oyo ya ce akwai bukatar yin wannan tunani saboda wasu mutane na da fassara daban-daban kan ziyararsa.
Ya ce:
“A wannan lokaci na siyasa, watakila akwai bukatar ka tambayi kanka kan dalilin da yasa akwai bukatar ka zo gidan gwamnati saboda mutane na iya yi masa wata fassarar. Amma ka aiko mini da sako kuma na yi farin cikin tarbarka a Ibadan."
2. Abun da kayi ya fi gaban siyasa
A wajen Makinde, kasancewar babban jigon na APC na kasa a jihar PDP irin Oyo ya nuna ya fi karfin siyasa da shingen da ta ke haifarwa a tsakanin al’ummar da suka fito daga yanki da al’adu guda.
Kalamansa:
"Muna matukar godiya da wannan ziyara kuma muna so ka sani cewa mun lura sosai cewa ka fi gaban siyasa da kuma duk abun da ke gudana a nan sannan ka zo ka kasance tare da mu a wannan lokaci da muke cikin bakin ciki. Muna godiya."
3. Muna yi maka fatan alkhairi a fafutukarka na neman shugabancin kasar
Gwamnan, a madadin jihar ya yi wa Tinubu fatan alkhairi a kudirinsa na son zama shugaban kasar Najeriya na gaba a 2023.
4. Mafi alkhairi muke so wa Najeriya
Sai dai, Makinde ya fada ma dan siyasar wanda ya bayyana kansa a matsayin masu nada sarki cewa yan Najeriya basu cancanci komai ba face nagartaccen shugaba a 2023.
Gwamnan ya ce:
"Bari na kuma yi amfani da wannan dama wajen yi maka fatan alkhairi a kudirin siyasarka na son jagorantar kasar nan. Muna so wa kasar mafi alkhairi kuma mafi alkhairi ne kadai ya dace a wannan lokaci."
Hular Tinubu ta yi daraja a kasuwar intanet, 'yan Najeriya sun yi tururuwa domin saye
A wani labari na daban, bayan ya ayyana aniyarsa na tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC), babban jigon jam'iyyar, Bola Ahmed Tinubu ya samu karbuwa a wajen wasu yan Najeriya.
A yanzu haka akwai wasu mutane da suka nuna ra'ayinsu na son siyar hularsa da ta shiga kasuwar intanet. Ana dai tallata hulunan ne a dandamalin sadarwa ta Twitter.
Wani mai amfani da dandamalin na Twitter @Jbmomoh, ya fada ma mabiyansa cewa yana da wasu huluna na siyarwa. Wadannan huluna ba kowanne bane face kwafin hular al'ada da tsohon gwamnan na jihar Lagas ke sanyawa.
Asali: Legit.ng