Aisha Buhari za ta karba bakuncin taron farko na PWC a Abuja

Aisha Buhari za ta karba bakuncin taron farko na PWC a Abuja

  • Mai dakin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari ta na shirin hada taron mata a karo na farko na jam’iyya APC Abuja
  • An samu bayanin ne a wata takardar wacce Hon. Abike Dabiri Erewa, shugaban kwamitinyada labarai na taron ya saki
  • Ana sa ran fiye da mata 1,000 daga jihohi 36 da kuma birnin tarayya, Abuja za su samu halartar taron, kuma mataimakiyar shugaban kasar Liberia za ta yi jawabi

FCT, Abuja - Uwar gidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari ta na shirin karbar bakuncin wani taron mata na farko na jam’iyyar APC a Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

Kamar yadda takardar ta zo, wacce Hon. Abike Dabiri Erewa, shugaban kwamitin watsa labaran taron ya saki, za a yi taron mai taken, “Murya daya mai kokarin samar da ci gaba.”

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Muhammadu Buhari ya dira jihar Ogun, ya fara kaddamar da ayyuka

Aisha Buhari za ta karba bakuncin taron farko na PWC a Abuja
Aisha Buhari za ta karba bakuncin taron farko na PWC a Abuja. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Hon. Stella Erhuvwa Okotee, mambar kwamitin rikon kwarya (CECPC)- wakiliyar mata, za ta jagoranci taron.

Daily Trust ta ruwaito cewa, kamar yadda takardar ta zo:

“Uwar gidan shugaban kasar Najeriya, Hajiya Aisha Buhari, za ta yi jawabi da farko. Mataimakiyar shugaban kasar Liberia, Chief Dr Jawel Howard-Taylor, za ta yi jawabi a kan irin abubuwan da ta fuskanta da gogayyar ta da ta yi a babban mukamin gwamnatin a taron wanda ake sa ran fiye da mata 1,000 daga jihohi 36 da babban birnin tarayya.”

Za a yi taron ne a ranar 18 da 19 ga watan Janairun 2022, a taron da za a yi a a dakin taron kasa da kasa da ke Abuja.

A cewar Dabiri-Erewa taron zai mayar da hankali musamman a bangarorin siyasa, shugabanci da sana’o’i.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Na shirya yin gaba da gaba da Tinubu a zaben fidda gwanin APC – Shahararren sanata

“Fiye da shugabanni 200 daga bangarorin gwamnati daban-daban da manyan mata ‘yan kasuwa da masu aiki a ma’aikatu za su halarci taron.
“Za su gabatar da bayanai don ba mata kaimi wurin siyasa, shugabanci da jagorantar kasuwanci," ta kara da cewa.

Tashar Africa Magic ta DSTV na shirin wasan kwaikwayo kan uwargidar Buhari

A wani labari na daban, Africa Magic, gagarumin kamfanin nishadantarwa mallakin MultiChoice, su na duba yuwuwar yin wasan kwaikwayo kan Aisha Buhari, uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Busola Tejumola, shugaban tashar ta Najeriya, ta bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da ta ke jawabi a taron kwana biyu da Africa Magic ta shirya na baje koli a jihar Kano, wanda aka kammala jiya.

A takardar da MultiChoice ta fitar, taron da ta shirya an samu ya hade da taron shekara- shekara na kungiyar watsa labarai na Najeriya, BON, ya samar da dama ga furodusoshi wurin mu'amala kai tsaye da Africa Magic domin samun damar tallatawa da siyar da hajojinsu.

Kara karanta wannan

Tuna baya: Wata 2 da suka gabata, Fashola yace Tinubu zai bayyana burinsa a watan Janairu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng