Hular Tinubu ta yi daraja a kasuwar intanet, 'yan Najeriya sun yi tururuwa domin saye

Hular Tinubu ta yi daraja a kasuwar intanet, 'yan Najeriya sun yi tururuwa domin saye

  • Kwafin hular Tinubu ta bayyana a kasuwar intanet, inda ta yi daraja da farin jini sosai
  • Tuni wasu yan Najeriya suka nuna ra'ayinsu na son mallakar wannan hula yayin da wani ya nemi a ajiye masa guda hudu
  • Hakan na zuwa ne yan kwanaki bayan babban jigon na APC ya ayyana aniyarsa na son takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023

Bayan ya ayyana aniyarsa na tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC), babban jigon jam'iyyar, Bola Ahmed Tinubu ya samu karbuwa a wajen wasu yan Najeriya.

A yanzu haka akwai wasu mutane da suka nuna ra'ayinsu na son siyar hularsa da ta shiga kasuwar intanet. Ana dai tallata hulunan ne a dandamalin sadarwa ta Twitter.

Kara karanta wannan

Yan siyasar kudu maso gabas 5 da ake sa ran za su fafata a zaben shugaban kasa a 2023

Hular Tinubu ta yi daraja a kasuwar intanet, 'yan Najeriya sun yi tururuwa domin saye
Hular Tinubu ta yi daraja a kasuwar intanet, 'yan Najeriya sun yi tururuwa domin saye Hoto: @Jbmomoh
Asali: Twitter

Wani mai amfani da dandamalin na Twitter @Jbmomoh, ya fada ma mabiyansa cewa yana da wasu huluna na siyarwa. Wadannan huluna ba kowanne bane face kwafin hular al'ada da tsohon gwamnan na jihar Lagas ke sanyawa.

Nan take sai mabiyansa suka fara martani. Wasu sun nemi a ajiye masu guda hudu yayin da wasu ke son sanin farashin hular.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ga martanin wasu mabiyan nasa da Legit Hausa ta tattara:

@Femiotunba1 ya ce:

"Da muka fada masu cewa, JAGABAN zai daidaita abubuwa, sun zata wasa muke yi, hular kadai za ta samar da daruruwan aikin yi, dan Allah ina bukata."

@yisawaliu ya ce:

"Ina fatan mu da muke Abuja za mu samu wasu?"

@mamatee001 ta yi martani:

"Shin mace na iya sawa?"

@Verified_Prince ya rubuta:

"Nawa farashin? Ina bukatar hudu daga ciki."

Kara karanta wannan

Addini, rashin lafiya, da matsaloli 5 da Tinubu zai fuskanta a neman Shugaban Najeriya

Burin Tinubu ya gamu da cikas na farko, Shugaban Yarbawan Afenifere ya ki mara masa baya

A gefe guda, mun ji cewa Shugaban kungiyar Yarbawa na kasa watau Afenifere, Ayo Adebanjo ya yi martani a game da shirin Asiwaju Bola Tinubu na takarar shugaban kasa.

Cif Ayo Adebanjo ya bayyana cewa kungiyar Afenifere ba za ta marawa wani ‘dan takara daya baya ba, har sai an canza tsarin mulkin kasar kafin 2023.

Adebanjo ya ce ba su yarda da tsarin mulkin da ake amfani da shi ba, don haka suke bukatar ayi gyara. Daily Trust ta fitar da wannan rahoto a ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng