Fitaccen dan jarida, Dele Momodu ya ayyana kudurin tsayawa takara a 2023 a PDP
- Fitaccen dan jaridan nan, Dele Momodu ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP
- Ya bayyana haka ne yau Alhamis a Abuja yayin da ya ziyarci ofishin shugaban PDP a babban birnin tarayya
- Ya zuwa yanzu, ba a san me suka tattauna ba, amma dai suna ganawar sirri a ofishin shugaban na PDP
Abuja - Shahararren dan jarida kuma mawallafin mujallar Ovation, Dele Momodu, a ranar Alhamis, 13 ga watan Janairu, ya je sakatariyar jam’iyyar PDP ta kasa domin bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.
Labari ya iso Legit.ng Momodu ya gana da shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyiorchia Ayu, domin bayyana burinsa ga jam’iyyar.
Sanye da babbar riga da hula, Momodu ya mika takardar neman tsayawa takarar shugaban kasa ga shugaban jam’iyyar PDP.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, Momodu yana cikin ganawar sirri da shugaban na PDP.
Bola Tinubu: Ba abin da zai hana ni zama shugaban kasa a zaben 2023 sai abu daya
Yanzu dai an tabbatar da cewa Asiwaju Bola Ahmed na daya daga cikin jerin masu son yin takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC don gadan kujerar shugaba Buhari.
Tinubu, wanda yake shugaban jam’iyyar APC na kasa ya tabbatar da hakan bayan ganawarsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a Aso Rock Villa a ranar Litinin, 10 ga watan Janairu.
A tattaunawarsa da manema labarai a ranar Litinin, tsohon gwamnan na jihar Legas ya bayyana cewa a matsayinsa na sarki a siyasa, babu abin da zai hana shi zama sarki shugaba sai dai idan ya yi kisan kai, inji rahoton The Cable.
A cewarsa:
"Babu wani abu da zai hana mai nada sarki zama sarki sai dai idan yayi kisan kai."
A wani labari, an yi hira da tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso a game da batun da yake ta yawo na komawarsa jam’iyyar APC mai mulki.
A wata tattaunawa da ya yi da gidan talabijin na Channels TV, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yace babu gaskiya a wannan jita-jita da yake ta yawo a yau.
A cewar Kwankwaso wanda ya yi gwamna a Kano, labarin karya ne kurum wasu suka kitsa. BBC ta fitar da wannan rahoto a ranar 9 ga watan Junairu, 2022.
Asali: Legit.ng