Ba motar hawa suke da shi ba sai yawan tambaya game da gadar sama da nake gina wa, Ikpeazu ya mayar da martani

Ba motar hawa suke da shi ba sai yawan tambaya game da gadar sama da nake gina wa, Ikpeazu ya mayar da martani

  • Gwamnan Jihar Abia ya mayar da martani kan wadanda ake tambayarsa game da gadar sama da gwamnatinsa ta fara gina wa shekaru 6 da suka shude
  • Gwamna Okezie Ikpeazu, cikin bacin rai, ya amsa cewa mafi yawancin masu tambaya kan yaushe za a kammala gadar ba su da motoccin hawa
  • Ya kuma kara da cewa babu wanda ya umurce shi ya gina gadar kawai shine ya duba ga lura cewa akwai bukatar a yi gadan don haka ya fara bada kwangilar aikin

Jihar Abia - Gwamna Okezie Ikpeazu na Jihar Abia ya ce mutane da dama wadanda ba su da motocin hawa ne suke tambayan inda aka kwana batun gadar sama (flyover) da gwamnatinsa ke gina wa.

Ikpeazu ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a baya-bayan nan a gidan rediyo kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Benue: Ɗan shekaru 44 ya cire ƴaƴan marainansa da kansa don daƙile tsabar sha'awarsa

Marasa motoccin hawa ne suke yawan tambaya game da gadar sama da na ke gina wa, Gwamna Ikpeazu
Gwamnan Abia ya ce mutanen da ba su da motoccin hawa ne ke tambaya game da gadar sama da ya ke gina wa. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Mai gabatar da shirin a gidan rediyon ya masa tambaya ne kan dalilin da yasa aikin ginin gadan ke daukan lokaci, duba da cewa tun shekaru shida da suka gabata aka fara aikin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Masu nace wa da tambaya kan aikin gadar mafi yawancinsu ba su da motoci, Ikpeazu

Amma, Ikpeazu, wanda bisa dukkan alamu bai ji dadin tambayar ba, ya ce shin ko wadanda suke neman bayanin ne suka saka shi gina gadan kamar yadda ita ma LIB ta ruwaito.

A cewarsa:

"Shin kai ne ka saka ni in gida gadan ta sama? Na fara ginin gadar ne don kashin kai na saboda na ga akwai bukatar hakan. Mafi yawancin wadanda suke neman jin inda aka kwana kan aikin ginin gadan ba su da motoccin hawa, da kafafunsu suke yawo. Menene hadinsu da gadar sama?

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan sanda sun shiga tsakani yayin da kwarto ya kashe mijin daduronsa

"Ya kamata su yi farin ciki cewa saura kadan mu kammala aikin gadar na sama; a halin yanzu muna aiki wurin turbar duwatsu na gadan ta sama"

Ikpeazu da mai masa tambayoyin sun yi magana ne da harshen Igbo.

Kalaman na gwamnan ya janyo cece-kuce a dandalin sada zumunta, inda wasu mutane da dama ke zarginsa da nuna banbanci tsakanin talakawa da masu hannu da shuni.

Gwamna ya kori surukinsa daga aiki, ya umurci kwamishina ya maye gurbinsa

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan Jihar Abia, Okezie Ikpeazu, ya sanar da korar surukinsa, Mataimakin Manajan, Hukumar Kare Muhalli ta JIhar Abia, ASEPA, ta Aba, Rowland Nwakanma, a ranar Alhamis, The Punch ta ruwaito.

A cikin wata takarda da sakataren gwamnatin jihar Abia, Barista Chris Ezem ya fitar, Ikpeazu ya kuma 'sallami dukkan shugabannin hukumar tsaftace muhalli a Aba amma banda na Aba-Owerri Road, Ikot Ekpene da Express.'

Kara karanta wannan

Gwamnatina ba za ta yi watsi da ku ba: Shugaba Buhari ya yi jajen kisan 'yan Zamfara

Amma gwamnan ya bada umurnin cewa dukkan 'masu shara ba a kore su ba, su cigaba da aikinsu na tsaftacce hanyoyi da tituna a kowanne rana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164