Tallafin Survival Fund: Kano da sauran jihohin da suka fi amfana da shirin

Tallafin Survival Fund: Kano da sauran jihohin da suka fi amfana da shirin

  • Jihohin Legas, Kano da Abia sune a sama wajen cin gajiyar shirin gwamnatin tarayya na tallafin Survival Fund
  • Karamar ministar masana’antu, kasuwanci da saka hannun jari, Maryam Katagum, ce ta bayyana hakan a taron kwamitin dorewar tattalin arziki
  • Katagum ta kuma ce nan ba da dadewa ba kowace jiha za ta samu akalla naira biliyan 1.7 daga dukka shirye-shiryen

Abuja - Lagas, Kano da Abia sune manyan jihohin da suka fi amfana daga shirin tallafi na Survival Fund da gwamnatin tarayya ta raba wa yan Najeriya inda suka samu naira biliyan 2.5, naira biliyan 2, da naira biliyan 1.7 kowannensu.

Hakan na kunshe ne a jawabin karamar ministar masana’antu, kasuwanci da saka hannun jari, Maryam Katagum, a taron farko na kwamitin dorewar tattalin arziki na 2022, jaridar Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kano: Matukan adaidaita sahu sun tafka asarar N300m bayan fadawa yajin aiki

Tallafin Survival Fund: Legas, Kano da sauran jihohin da suka fi amfana da shirin
Tallafin Survival Fund: Legas, Kano da sauran jihohin da suka fi amfana da shirin Hoto: Professor Yemi Osinbajo
Asali: Facebook

Babban mai ba mataimakin shugaban kasa shawara kan harkokin labarai, Laolu Akande, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin, 11 ga watan Janairu, a cikin wata sanarwa da ya fitar.

A jawabinta kan shirin tallafin, Katagum ta bayyana cewa yayin da dukka jihohin tarayya suka samu kaso daban-daban na asusun tallafin na N75bn tare da shirye-shiryensa daban-daban, daga karshe kowace jiha za ta samu akalla naira biliyan 1.7 daga dukkan shirye-shiryen.

Ta kuma bayyana cewa jihohin Lagas, Abia da Kano sun ketare iyaka, inda Lagas ta kai sama da naira biliyan 2.5 sannan Kano ta kai sama da naira biliyan 2. Babu jihar da ta karbi kasa da naira biliyan 1 zuwa yanzu, rahoton Punch.

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, wanda ya jagoranci taron kwamitin ta yanar gizo a ranar Litinin a fadar shugaban kasa, ya karbi rahotanni daga ministoci da shugabannin hukumomin tarayya kan ci gaban wajen aiwatar da tsarin dorewar tattalin arziki na gwamnatin Buhari.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Ganduje ta haramta Cakuduwar maza da mata a wurin ninkaya, luwadi, Madugo da wasu sabbin dokokin biki

Buhari: Sai bayan na sauka 'yan Najeriya za su gane irin gatan da na yi musu

A gefe guda, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce za a ji tasirin aikin da ya tafka a Najeriya bayan ya bar ofis a zaben 2023, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban ya fadi haka ne bayan kaddamar da sabuwar gudanarwar Hukumar Zuba Jari ta Najeriya (NSIA).

A takaitaccen biki da aka gudanar a fadar gwamnati, Abuja, Buhari ya umarci hukumar da ta kara saka hannun jari da ke tallafawa fadada tattalin arziki, saboda an yi hasashen farashin mai na duniya zai ragu zuwa kusan dala 40 a kowace ganga nan da shekarar 2030.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng