2023: Abin da Ohanaeze ta ce game da niyyar fitowa takarar Tinubu matsayin shugaban kasa

2023: Abin da Ohanaeze ta ce game da niyyar fitowa takarar Tinubu matsayin shugaban kasa

  • Kungiyar Igbo ta Ohanaeze na neman sanin ko ƙudirin Tinubu na yin shugabancin ƙasa ya yi daidai
  • Ƙungiyar ta ƙabilar Igbo ta bayyana Tinubu a matsayin adali kuma mai hangen nesa tare da bashi shawara
  • Ƙungiyar ta bayyana cewa lokaci yayi da ɗan ƙabilar Igbo zai jagoranci Najeriya

Babbar ƙungiyar gamayyar ƙabilar Igbo a Najeriya, Ohanaeze Ndigbo, ta bayyana Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin mai hangen nesa kuma mai sanin ya kamata.

Sai dai, duk da haka, ƙungiyar ta ce yanzu lokaci ne da ɗan yankin kudu maso gabas ya dace ya zama shugaban kasar Najeriya, rahoton The Nation.

2023: Abin da Ohanaeze ta ce game da niyyar fitowa takarar Tinubu matsayin shugaban kasa
2023: Tinubu mutum ne mai hangen nesa kuma adali amma a yanzu Igbo ya kamata ya zama shugaban Najeriya, Ohaneaze. Hoto: The Nation
Asali: Depositphotos

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

2023: Ƴan Najeriya na son PDP ta karɓi shugabancin ƙasa daga hannun APC, Wike

Ƙungiyar, a wata sanarwa da ke maida martani kan matsayar Tinubu na neman takarar shugabancin ƙasa, ta nemi ba'asin ko hakan anyi adalci da daidaito.

Da yake zantawa da wakilin The Nation, mai magana da yawun Ohanaeze Ndigbo, Alex Ogbonnia, ya bayyana Tinubu a matsayin mutum mai adalci da sanin abun da ya kamata.

Ogbonnia ya ce:

"kowanne ɗan Najeriya ya kwana da sanin cewa ana karɓa-karɓa ne na kujerar shugabancin ƙasa tsakanin Kudu da Arewa. Amma a wannan lokacin ba wai Kudun ba, amma Kudu maso gabas. Muna da ƙwarin gwuiwar za a yi adalci. Kuma adalci shine ɗan ƙabilar Igbo ya zama shugaban ƙasa a 2023.
"Ana ragamar duniya ne da hangen nesa, daidaito da adalci. A taƙaice, daidaito da adalci sune manyan ginshiƙan da ke tabbatar da ɗorewar duk wani tsari."

Ya cigaba da cewa:

"Shin ƙudirin Tinubu na kan adalci da daidaito? Ga duk wani abu da ake bukatar yin nasara, dole ya tafi akan adalci da daidaito. Mu a matsayar mu a Ohanaeze, duk wani ƙudiri da ya saɓa da adalci matacce ne. Baza a taɓa nasara ba. Wanda suka gwada a baya sun sani ba abu ne mai yiwuwa a cimma abun da yake ba adalci ba, ba a yin nasara. Tarihi ya tabbatar da rashin adalci baya ɗorewa.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Jam'iyyar APC ta maida zazzaafan martani ga kalaman Tinubu na takarar shugaban ƙasa a 2023

"To, an san Tinubu a matsayin mutum mai hangen nesa a baya kuma ya sha nuna hakan ta hanyoyi da dama.
"Idan ya dawo ya fara saɓawa daga wannan ya saka kansa a abubuwan rashin adalci da son kai, hakan zai karya lagon sa."

Hadimin Buhari: Surutai da barazana ba zai sa Arewa ta mika wa kudu shugabancin kasa a 2023 ba

A wani labarin daban, tsohon hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari a bangaren harkokin Majalisar Wakilai, Abdulrahman Suleman Kawu Sumaila, ya ce arewa ba za ta bar wa kudu shugabancin kasa ba saboda tsoratarwa da surutai, Daily Trust ta ruwaito.

Ya yi wannan maganar ne yayin mayar da martani a kan wata magana da Ministan Kwadago, Chris Ngige ya yi inda ya ce duk wata jam’iyyar da ta tsayar da dan arewa za ta fadi zaben shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164