Shugabanci a 2023: Kwankwanso ya bayyana dalilin da yasa ba za a ba 'yan kudu dama ba
- Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana dalilin da zai sa ba za a ba Kudu damar takarar shugaban kasa a 2023 ba
- Ya bayyana haka ne yayin wata hira da yayi da gidan talabijin na Channels a jiya Lahadi 9 ga watan Janairun 2022
- Hakazalika, Kwankwaso ya yi bayanai da dama da suke da alaka da siyasar Kano da jam'iyyar PDP a dunkule
Jihar Kano - Premium Times ta tattaro cewa, tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce ba ya son a kai tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a 2023 zuwa Kudancin Najeriya.
Kwankwaso ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da gidan Talabijin na Channels a daren Lahadi inda ya kuma yi magana kan matsalolin siyasa da dama gabanin zaben 2023.
A nasa muhawarar, ya yi Allah wadai da dagewar da kungiyar gwamnonin kudancin kasar ta yi a watan Yulin 2021 na cewa dole ne shugaban kasar ya fito daga yankinsu ta kowace hanya.
Ya dauki kiran da gwamnonin da sauran shugabannin suka yi a matsayin wani yunkuri na tsorata yankin Arewa domin ya sauke kudurin tsayawa takara.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kwankwaso ya ce kamata ya yi a yanke shawarar tsayawa takara bisa dabaru ba wai ta hauragiya ko son kai ba.
Da yake kafa hujjarsa, Kwankwaso ya ce:
“Kunga mutane su na cakuda abin da bai kamata a cakuda ba. Mu na da jam’iyyu daban-daban, inda kowace jam’iyya za ta kai takara, ya ragewa dabararta.
"Idan aka yi duba zuwa 2023, jam’iyyar APC tayi mulkin shekara takwas, PDP kuma tayi 16. A cikin 16 da PDP tayi, Kudu tayi shekara 14, Arewa tayi biyu."
A halin da ake ciki dai, jam’iyyar APC ko PDP babu wacce ta sanar da wa za ta ba tikitin takarar shugaban kasa a zaben mai zuwa.
Jinkirin da manyan jam'iyun kasar biyu suka yi na tsayar da dan takara ya janyo cece-kuce kan cewa za su iya jefa tikitin ga dukkan masu son tsayawa takara.
Karya ake yi mani kan batun komawa APC
A hirar, tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso yayi magana game da batun da yake ta yawo na komawarsa jam’iyyar APC mai mulki.
A wata tattaunawar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yace babu gaskiya a wannan jita-jita da yake ta yawo a yau.
A cewar Kwankwaso wanda ya yi gwamna a Kano, labarin karya ne kurum wasu suka kitsa. BBC ta fitar da wannan rahoto a ranar 9 ga watan Junairu, 2022.
Asali: Legit.ng